Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai
Wata uku dalibin mai shekara 13 yana zuwa makarantar da bindiga yana barazanar harbin abokan karatunsa
![Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2019/02/Bindiga.jpg)
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita.
Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom.
A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron.
DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta.
- An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji
- Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata
Ta bayyana cewa ya shaida musu cewa tun a watan Nuwambar shekarar 2024 ya ɗauko bindigar daga kwabar tufafi da ke ɗakin mahaifinsa yake amfani da ita.
Ta ce bayan samun rahoto ne, “ba tare da ɓata lokaci ba rundunar ta garzaya ta kama yaron tare da ƙwace bindigar hannun, wadda ƙirar gida ce.
“A yayin bincike yaron ya shaida mana cewa tun watan Nuwambar 2024 bindigar take hannunsa, kuna ya dauko ta ne daga kwabar mahaifinsa, wanda shi ma daga bisani muka kama shi, muna bincikar su tare.”
Ɗan shekara 60 ya lalata ’yar shekara 9
Ta ce rundunar ta kuma cika hannu da wani ɗan shekara 60 da ya yi wata yarinya mai shekara tara a duniya fyade.
Ta ce dubun tsohon ta cika ne bayan mahaifiyar yarinyar ta kai ƙara a ofishin ’yan sanda daga ƙauyen Afaha Offiong, da ke yankin Nsit Ibom.
Jami’ar ta bayyana wa ’yan sanda cewa bayan ta aiki ’yar tata ne tsohon ya tare ta ya shigar da ita cikin jeji ya keta matuncinta, inda daga baya ya ba ta Naira 200.
Daga bisani jami’an rundunar suka je suka cika hannu da shi kuma nan gaba za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.