Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya
Bayan kammala binciken yaran, bincike ya nuna cewa an yi lalata da yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10.

Fyade
Ana zargin wani matashi da yin lalata da yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa a yankin Zariya.
Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna.
- Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya
- Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa
Daraktan Cibiyar Salama da ke Asibitin Gambo Sawaba, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar Mata a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna Oguchwku Cibiyarsu tare da wasu yaran Makarantar Firamare ta Jafaru LEA su biyu.
Daraktar ta ce, bayan kammala binciken yaran, sakamakon ya nuna cewa an yi lalata da su.
Daraktan cibiyar Hajiya Aishatu Ahmad ta ce, sun ɗora yaran a kan magani, kuma sun ba ’yan sanda sakamakon, tare da tura ƙwafin sakamakon zuwa ga Kwamishinar Jinƙai da Walwala ta Jihar Kaduna domin ɗaukar mataki.
Babban jami’i a ofishin ’yan sanda na Kasuwar Mata ya ce “duk da taƙaddama akan rashin yarda da sakamakon binciken da Asibitin Gambo Sawaba da iyalan wanda ake zargin suka yi, sai na sake tura su asibitinmu na musamman domin ƙara binciken kuma yanzu haka mun tura su zuwa Kaduna.”
Duk ƙoƙarin kiran wayar, mai magana da yawan rundunar ’yan Sanda na Jihar Kaduna ASP Mansur Hassan, tare da tura masa rubutaccen saƙo, amma har zuwa wannan lokacin bai amsa ba.