Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

Haruna Danyaya ya zama Sarki na 16 da ya ɗare karagar mulki a Ningi.

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta amince da naɗin Alhaji Haruna Yunusa Muh’d Danyaya, a matsayin sabon Sarkin Ningi.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Ningi/Warji, Adamu Hashimu Ranga, ya taya al’ummar Bauchi da masarautar Ningi murnar naɗin sabon sarkin.

Danyaya, ya zama sarki ne bayan rasuwar mahaifinsa, Dokta Yunusa Danyaya, wanda ya rasu yana da shekara 88.

Ya rasu a ƙasar Saudiyya a ranar 22 ga watan Agusta.

Ranga, ya jinjina wa gwamnan jihar naɗin Danyaya a matsayin Sarkin Ningi na 16, inda ya bayyana cewar an saka ƙwarya a burminta.

Ya kuma bayyana gamsuwarsa da cewa sabon Sarkin zai ci gaba da irin ayyuka irin na mahaifinsa, wanda aka san shi da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ɗan majalisar ya buƙaci sabon Sarkin da ya ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya, domin ci gaba da inganta zaman lafiya, had6in kai, adalci, da kuma ci gaban tattalin arziƙin al’ummar Ningi da Jihar Bauchi baki ɗaya.

Kafin naɗinsa, Haruna Danyaya, ya kasance Chiroman Ningi kuma babban ɗan marigayi Dokta Yunusa Danyaya.