Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto

A cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali.

Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto

Wani ɗan Nijeriya ɗan asalin Jihar Yobe, Saidu Abdulrahman, ya lashe kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya a matsayin mafi ɗaukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya.

Bayanai sun ce a cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali a watan Satumba na bara, lamarin da ba shi damar doke wanda ya lashe kambun na bara da hotuna 500.

Da wannan ƙwazo ne Kundin Bajinta na Duniya wata Guinness World Records (GWR) ya karrama matashin da lambar yabo.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, matashin ya bayyana cewa, “ina mai farin cikin sanar da cewa, an karrama ni a hukumance da matsayin mai riƙe da kambun tarihi na Guinness saboda na mafi ɗaukan hotunan da yawa waɗanda na ɗauka cikin sa’a ɗaya!

Saidu Abdulrahman riƙe da kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya

“Karɓar shaidar lashe lambar yabo ta kudin Guinness World Records, sakamako ne na jajircewa ta da kuma goyon baya mara iyaka daga dangina da abokaina, da jagororina, da masu yi min fatan alkhairi waɗanda suka kasance tare da ni.”

Ya ce “Nasarar kafa wannan tarihi na ɗaukar hotuna 897 a cikin minti 60 kacal, ba tawa ce ni kaɗai ba; ta duk ɗan Nijeriya ce da ya amince da ni, ya taimaka min, ya kuma jinjina min tun daga lokacin da na fara har gama.”

“Kafa wannan tarihi shaida ce ta cewa za mu iya yin bajinta a duniya.”

Haka ita ma cikin wani saƙo da Kundin Bajintar ya wallafa, ya ce “Abdulrahaman ya yi yunƙurin kafa tarihin ne domin wayar da kan jama’a game da ɗaukar hoto a Nijeriya.

TRT dai ya ruwaito cewa an ba shi lambar yabon ce a garin Potiskum da ke Jihar Yobe, kana taron ya samun halartar jami’an gwamnatin jihar da ɗalibai da kuma masoyansa.

Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa

Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa

Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi

Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato