Ɗan Sanda cikin maye ya saki masu laifi 13 don murnar sabuwar shekara

Waɗanda aka tsare 13 an zarge su da laifuffuka da suka haɗa da cin zarafi, fashi da kuma sata.

Ɗan Sanda cikin maye ya saki masu laifi 13 don murnar sabuwar shekara

Hoto daga Channels TV

Wani jami’in ɗan sanda da ya bugu da barasa a Zambiya ya kuɓutar da wasu mutane 13 da ake tuhuma aka tsare su a sel domin su je yin bikin sabuwar shekara, kamar yadda jami’an suka sanar.

Wani rahoto da BBC ta fitar ya ce an kama sufeto Titus Phiri bayan ya saki waɗanda ake zargin daga sel din ofishin ‘yan sanda na Leonard Cheelo da ke babban birnin ƙasar, Lusaka kafin ya gudu da kansa.

Waɗanda aka tsare 13 an zarge su da laifuffuka da suka haɗa da cin zarafi, fashi da kuma sata.

A halin yanzu dai dukkansu sun gudu kuma an fara farautarsu domin gano inda suke.

Kakakin ‘yan sanda Rae Hamoonga ya ce, jami’insu Phiri, “yana cikin yanayi na maye, ya karɓe makullan sel ɗin daga ɗan sanda Serah Banda a jajibirin sabuwar shekara.

“Daga baya, Insfekta Phiri ya buɗe ƙofofin da aka tsare maza da mata kuma ya umurci waɗanda ake zargin da su fice, yana mai cewa suna da ‘yanci su fita don yin murnar sabuwar shekara,” in ji shi.

“A cikin mutane 15 da ake zargi, 13 sun tsere. Bayan faruwar lamarin, ɗan sandan ya gudu daga wurin.”

Har yanzu Mista Phiri bai ce uffan ba kan zargin da ake tuhumarsa.