Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

Rahotanni sun nuna cewar jami’in ya shiga wani ɗaki sannan ya sa bindiga ya harbe kansa har lahira.

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

Wani Jami’in Ɗan Sanda da ke aiki a ofishin ’yan sanda na yankin Mada a Jihar Nasarawa, ya harbe kansa da bindiga har lahira.

An gano ɗan sandan, mai suna Dogara Akolo-Moses, yana aiki ne a Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon lokacin da ya kawo ƙarshen rayuwarsa.

Shaidu sun bayyana cewar ya shiga wani ɗaki sannan ya harbe kansa da bindiga.

Sautin harbin bindigar ne ya jawo hankalin abokan aikinsa, waɗanda suka garzaya zuwa ɗakin, inda suka same shi kwance cikin jini da bindiga a gefensa.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya hallaka kansa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar tana gudanar da bincike don gano abin da ya sa jami’in ya ɗauki wannan mummunan mataki.

Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara