Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja
Kakakin rundunar ya ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa jami’in ya rataye kansa ba.
![Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/whatsapp-image-2025-02-09-at-5.03.34-am-e1739127006772.jpeg)
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira.
Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar.
- Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu
- Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari
An tsinci gawarsa rataye a cikin dakinsa.
Majiyoyi sun ce mahaifinsa, Malam Usman Bawa ne, ya fara gano abin da ya faru sannan ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Kontagora.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce: “A ranar 8 ga watan Fabrairu, 2025, da misalin karfe 2 na rana, an samu rahoton cewa ASP Shafi’u Bawa na Rundunar 61 PMF, Kontagora, ya rataye kansa.
“Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya aikata hakan ba.
“An dauke gawarsa tare da mika ta ga iyalansa domin yi mata jana’iza.
“Ana ci gaba da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.”