Ɗan sanda ya saki ’yan fashi 13 saboda murnar Sabuwar Shekara

Wani ɗan sanda da ke cikin maye ya saki wasu tsararru 13 da ake zargi da fashi da makami domin su yi bikin Sabuwar Shekara.

Ɗan sanda ya saki ’yan fashi 13 saboda murnar Sabuwar Shekara

Wani ɗan sanda da ke cikin maye ya saki wasu tsararru 13 da ake zargi da fashi da makami domin su yi bikin Sabuwar Shekara.

Insfekta Titus Phiri, ya ƙwace makullin del din da ’yan fashin da suke kulle ne, ya buɗe sannan ya umarce su san inda dare ya yi musu.

Wannan lamari ya faru ne a a jajibirin ranar Sabuwar Shekara a ofishin ’yan sanda na Leonard Cheelo da ke birnin Lusaka, na ƙasar Zambia.

Rahotanni sun ce bayan tserewar tsarrarun da ake tuhuma da manyan laifuka, Insfekta Phiri ya cika wandonsa da iska.

A halin yanzu dai jami’in ya shiga hannu a yayin da ’yan sanda ke ci gaba farautar gudaddun mutanen.

Irin haka ta taɓa faruwa a kasar a shekarar 1997, inda wani ya ba da umarnin sakin wasu tsararru 53 ba tare an gurfanar da su ba.