Ɗan Sanusi II ya auri ’yar babban ɗan siyasa a Arewa

Bikin ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da jami’an gwamnati.

Ɗan Sanusi II ya auri ’yar babban ɗan siyasa a Arewa

Ɗan Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, Ashraf Adam Lamido, ya auri masoyiyarsa, Sultana Nazif, ’yar fitaccen ɗan siyasa daga Jihar Bauchi, Sanata Suleiman Mohammed Nazif.

Auren ya gudana a Masallacin Ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ƙanwar angon, Fulani Siddika ce, ta wallafa hotuna da bidiyon auren a shafin Instagram.

Manyan mutane da dama, ciki har da jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya, sun halarci bikin.

Ga hotunan yadda bikin ya gudana:

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja