’Yan bindiga sun binne gawar Sarkin Gobir —Ɗansa

’Yan bindiga sun sako shi bayansa suka ƙarbi kuɗin fansa da kuma babura bayan da farko sun yi wa mahaifinsa kisan gilla

’Yan bindiga sun binne gawar Sarkin Gobir —Ɗansa

Ɗan Sarki Gobir da ’yan bindiga suka sace tare da mahaifinsa, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da su.

Babban ɗan sarkin, Surajo Isa, ne ya tabbatar wa wakilinmu hakan a Sakkwato a daren Laraba.

Surajo ya ce, “ƙanen namu da aka sako ya shaida mana cewa ’yan bindigar sun binne gawar mahaifinmu, bayan da suka kashe shi.”

Ya bayyana cewa, “Sun dawo gida daga maɓoyar ’yan bindiga ne da misalin ƙarfe 8.30 ma dare,” kamar yadda ya shaida wa wakilin namu.

Ya bayyana cewa an sako ƙanen nasa ne bayan ’yan bindigar sun karɓi kudin fansa da kuma baburan da suka buƙata.

’Yan bibdiga sun sako shi ne bayan kisan gilla da suka yi wa mahaifinsa, Alhaji Isa Muhammad Bawa a ranar Talata.