Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88

Zolaya ce, ba su fahimci cewa, duk da bambancin shekaru, za mu iya son junanmu.

Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88

Ma’aurata da ke da tazarar shekaru 45 sun shawo kan masu zolayarsu da batun kiwon lafiya don samun farin ciki na musamman a baya kuma sun ce sun ki jin kunyar waɗansu ba su fahimci alakar aurensu ba.

Ma’auratan sun shawo kan matsalar da za ta iya shafan huldarsu da wadanda ke son raba aurensu – amma duk da haka sun nace za su yi iya kokarinsu don hana su farin ciki a rayuwar auren.

Adrián Narbáez, mai shekara 43 yanzu ya hadu da matarsa Delia Lúkuez mai shekara 88, a wani baje kolin fasaha a shekara ta 1998, tun yana dan shekara 16, ita kuma tana da shekara 61.

Da farko, ma’auratan abokai ne kawai, saboda sun hada kai a kan abubuwan da suke so kan kirkirar fasaha.

Malama Delia ta kasance kwararriya mai sha’awar fentin, yayin da Adrián yake son rubutun wakoki da tatsuniyoyi.

Bayan haduwarsu ta farko, Adrián da Delia sun ci gaba da tuntubar juna, suna musayar wasiku, wanda Adrián yake yi har yau.

Yayin da shekaru suka shige, abokantakarsu ta zama soyayya, kuma Adrián, wanda yake jin kamar an haife shi a lokacin da bai dace ba, ya fada wa Delia cewa yana son ta.

Dangantakarsu ta yi danko, amma tsawon wata 12, sun zabi su boye soyayyarsu—suna haduwa lokaci zuwa lokaci.

Ma’auratan, wadanda suke zaune a garin Ribadabia, Mendoza da ke Argentina, sun bi ka’idojin addininsu kuma ba su iya kadaita da juna a wani wuri ba.

Haka kuma sun ta cin karo da kalubale da zarar sun yanke shawarar fitowa fili da soyayyarsu.

Kamar yadda Delia ta bayyana wa manema labarai na gida, ba kowa ne ke farin ciki game da dangantakarsu ba.

Ta bayyana cewa: “Mahaifin mijina ya karbe ni nan da nan, amma mahaifiyarsa ba ta so.”

Adrián, wanda ya ce ya fi son tsofaffin samfuran mota da gidaje, ya kara da cewa: “Zolaya ce, ba su fahimci cewa, duk da bambancin shekaru, za mu iya son junanmu. Da farko, sun yi duk mai yiwuwa domin su raba mu.”

Amma duk da manyan matsalolin da suka fuskanta, kaunar junansu ta yi nasara a karshe.

Adrián, wanda kodayake matashi ne, bai taba sha’awar mata masu irin shekarunsa ba, inda ya bayyana wa kafar yada labarai ta Infobae cewa: “Ban taba jin kunyar bambancin shekarun ba.

“A gaskiya, ban lura da shi ba. Kuma kodayake akwai shekaru 45 a tsakaninmu, ina tafiya tare da ita ko’ina.

Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno 

’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci

Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata

Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba