Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Wani direba ɗan shekara 60 ya rasu bayan ya faɗa a cikin rijiya a kan titin Haɗeja Road da ke Kano.

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Rijiyar Bajimba: Wadda ake dibar ruwa daga karfe 12 na dare zuwa 6 na safe Hoto daga Magaji Isah

Wani direba ɗan shekara 60 ya rasu bayan ya faɗa a cikin rijiya a Kano.

Dattijon, mai suna  Sabi’u Unguwa Uku, wanda direban matar wani tsohon minista ne ta gamu da ajalinsa ne a rukunin gidajen ma’aikatan Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke kan titin Haɗeja Road da ke Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya ce tsautsayi ya ritsa da direban ne “bayan da ya sauke wasu baƙi a wani gida da ke kusa da abin ya faru.

“Ya fito ne domin yin fitsari, bai sani ba, ashe akwai wata tsohuwar rijiyar da ba a amfani da ita.”

Ya ce bayan samun kiran gaggawa kan lamarin jami’an hukumar sun isa wajen suka ceto mutunin, suka kai shi Asibitin Sir Sanusi, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa.

Jami’in ya bayyana cewa an kai gawar a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke unguwar Dakata.