Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m
Fiye da rabin al’ummar yankuna 23 sun tsere domin kauce wa harin ɗan ta’adda Dogo Giɗe idan kuɗin da ya nema ba su samu ba
Al’ummar yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara na tserewa daga gidajensu saboda harajin Naira miliyan 100 da ƙasurgumin ɗan ta’adda Dogo Giɗe ya ƙaƙaba musu.
Mutanen ƙauyuka 23 da abin ya shafa suna gudun hijira ne domin tsira da ta rayuwarsu daga harin ɗan ta’addan bai samu kuɗin da ya buƙata ba.
Wani ɗan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da ya nemi a ɓoye sunansa ne ya tabbatar mana da cewa “fiye da rabin mutanen ƙauyukan sun riga sun tsere, sakamakon harajin da Dogo Giɗe ya sanya wa yankunan.
“Gaskiya hare-haren sun ragu a baya-bayan nan, amma dai suna tasar mutane inda suke ƙaƙaba musu haraji,” in ji ɗan Majalisar.
- An kori jami’an EFCC 27 daga aiki da saboda almundahana
- An ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su a Sakkwato
Aminiya ta gano cewa yankunan da shugaban ’yan bindigar ya sanya wa tarar suna yankin Gabashin Ƙaramar Hukumar Tsafe ne, inda ya sa musu daga Naira miliyan 2.7 mafi ƙarancin, zuwa miliyan 20.
Wani mazaunin ƙauyen Magazu mai suna Yusuf Dalhatu wanda ya yi ƙaura zuwa Gusau, ya shaida wa wakilinmu cewa yawancin mutanen ƙauyen sun riga sun tsere. Ya bayyana cewa dan uwansa da iyalansa sun koma garin tsari saboda rashin tabbas.
“A kowane lokaci ’yan ta’adda na iya zuwa karɓar kuɗin kuma idan ba su samu ba za su tashi jama’a,” in ji Malam Yusuf ta wayar tarho.
Shi ko Malam Isa Inuwa Maciya da ya yi ƙaura daga ƙauyen Maciya ya ce, “garinmu babu kowa yanzu. Lokacin da na baro magidanta huɗu ne kacal suka rage, su na suna shirin barowa. Sun riga tura iyalansu zuwa wurare da wannan abin tashin hankali bai shafe su ba.”
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mohammed Shehu, ya ce ya samu rahoto “cewa hatsabibin jagoran ’yan ta’adda Dogo Giɗe ya sanya wasu al’ummomi haraji. Duk da cewa mu da labarin mutane na tserewa amma akwai yiwuwar hakan, saboda idan ba su biya kuɗin ba ’yan ta’addan na iya kai musu hari.”
Ya ce jami’an tsaro ba za su made hannu ’yan ta’adda su rika cin karensu babu babbaka ba a kan al’umma, don haka ya ba da tabbacin girke jami’an tsaro domin daƙile harin.