Ɗan Takarar Gwamnan NNPP A Gombe Ya Fice Daga Jam’iyyar

Jagora Jam’iyyar NNPP kuma dan takaranta na Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2023, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya fice daga cikinta.

Ɗan Takarar Gwamnan NNPP A Gombe Ya Fice Daga Jam’iyyar

Jagora Jam’iyyar NNPP kuma dan takaranta na Gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2023, Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki, ya fice daga cikinta.

Mailantarki ya sanar da ficewar tasa ne a cikin wata takarda da ya aike wa shugaban NNPP na unguwar Herwagana a ranar Alhamis, mai ɗauke da kwanan watan jiya Laraba 10 ga watan Yuli na shekarar 2024.

Ya kuma turawa da kwafin takardar zuwa ga madugun NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa da kuma na jiharsa ta Gombe.

Mailantarki, ya gode wa shugabannin NNPP da mambobinta bisa adamar da suka ba shi ya bada gudunmuwarsa ga jam’iyyar musamman a lokacin babban zaɓen 2023.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC