Ɗan wasan Juventus Federico Chiesa ya koma Liverpool

Liverpool ta tabbatar da cewa Chiesa zai goya riga mai lamba 14 a Anfield.

Ɗan wasan Juventus Federico Chiesa ya koma Liverpool

Liverpool ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaba, Federico Chiesa daga Juventus ta Italiya kan fan miliyan 10.

Cikin ƙunshin yarjejeniyar, Liverpool za ta biya ƙarin fam miliyan 2.5 idan ɗan wasan ya yi ƙoƙari sosai.

Chiesa mai shekara 26 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara huɗu, kuma shi ne na farko da mai horarwa, Arne Slot ya ɗauka tun bayan zuwansa Anfield.

Ɗan wasan na gaba na cikin taurarin da suka doke Ingila a bugun finareti na wasan ƙarshe a gasar ƙasashen Turai ta Euro 2020 da suka fafata a filin wasa na Wembley.

Liverpool ta tabbatar da cewa Chiesa zai goya riga mai lamba 14, kamar yadda yake a ƙasarsa ta Italiya.

Liverpool ta samu nasarar ɗaukar Chiesa bayan takara da Barcelona wadda ta yi ƙasa a gwiwa wajen cimma yarjejeniya sakamakon rashin kuɗi da take fama da shi shekarun nan.

Juventus ta yi gaggawar cefanar da Chiesa saboda gudun kada ya tafi a ɓagas a ƙarshen kakar wasannin da aka soma, la’akari da cewa kwantaragin shekara ɗaya kacal ya rage masa da ita.