1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato

Tsohon Kwamishinan ya musanta masaniya kan sayar da hannayen jari da gwamnatin jihar ta yi.

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato

Tsohon Kwamishinan Kuɗi na Jihar Sakkwato, Alhaji Abdussamad Dasuki, ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike na Jihar, kan zargin karkatar da Naira biliyan 16.1 ƙarƙashin Gwamnatin Tsohon Gwamnan Jihar, Aminu Waziri Tambuwal.

Dasuki, wanda yanzu ke wakiltar mazaɓar Tambuwal-Kebbe a Majalisar Tarayya, ya ce bai san da Naira biliyan 16.1 da aka samu daga sayar da hannayen jarin gwamnatin jihar ba, wanda Kamfanin Zuba Jarin Jihar Sakkwato ya sayar.

Sai dai ya ce kamfanin kai-tsaye yake tura rahotonsa zuwa gidan gwamnatin jihar.

Dasuki, wanda ya riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi daga watan Yuni 2019 zuwa Maris 2022, ya ce bai san adadin hannun jarin da aka sayar ba.

Amma ya ce ya taɓa ganin wata takarda da ta bayyana cewa kuɗin hannun jarin ya kai sama da Naira biliyan uku.

“A lokacin da na zama Kwamishinan Kuɗi, kamfanin zuba jarin ne ke da iko a kan hannayen jarin. A lokacin annobar COVID-19, duniya na cikin matsala, kuma a ƙarshen watan Janairun 2020, aka umarce mu da fara biyan mafi ƙarancin albashin Naira 30,000.

“Yawancin jihohin Arewa sun rage albashi, amma Sakkwato ba ta rage ba, duk da ƙarancin kuɗin da ake samu daga asusun tarayya.”

Ya ƙara da cewa, “Mun kira kamfanin zuba jarin saboda wannan matsala. Mun yi taro da daraktan kamfanin, wanda ya sanar da ni cewa jimillar darajar hannayen jarin ya kai sama da Naira biliyan uku. Mun rubuta wa Gwamna wasiƙar neman izinin cire Naira biliyan biyu daga hannayen jarin domin taimaka wa ayyukan gwamnati da kuma biyan albashi.

“Gwamna ya amince, amma kamfanin sai ya tura Naira biliyan 1.5 zuwa asusun Babban Akanta, ba Naira biliyan biyu kamar yadda muka nema ba.

“Sun fara aiko Naira biliyan ɗaya, daga bisani kuma suka ƙaro Naira miliyan 500.”

Dasuki ya ce ba shi da masaniyar lokacin da aka sayar da hannayen jarin, domin kamfanin na kai rahotonsa kai-tsaye zuwa gidan gwamnati.

Dasuki, ya kuma ce ba zai iya tuna yawan albashi da kuɗin alawus ɗin ma’aikata a wancan lokacin ba.

Da lauyan kwamitin, Amanze F. Amanze, ya tambaye shi ko yana mamakin cewa kuɗin hannayen jarin ba Naira biliyan uku ba ne, Dasuki ya amsa da cewa, “Ban sani ba.”

Babban Akanta na jihar, Umar Ahmed Balarabe, da Babban Sakataren Jihar, Alhaji Malami Abdullahi Yabo, su ma sun bayyana a gaban kwamitin.

Babban Akantan, ya goyi bayan takardar bayaninsa, yayin da Babban Sakataren ya miƙa wasu takardu kan batun, wanda lauyoyin tsohon Gwamna Tambuwal da Dasuki suka yi watsi da su tun da farko, amma daga baya kwamitin ya amince da su.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato