12 ga Yuni: Buhari ya rattaba hannu akan ranar hutun ma’aikata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar hutun ma’aikata na kowace shekara wanda kuma ita ce aka amince da ranar Dimokaradiyya. Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Sanata Ita Enang, ne ya bayyanawa wakilinmu hakan yau Litinin. Sanata Ita, ya ce an […]

12 ga Yuni: Buhari ya rattaba hannu akan ranar hutun ma’aikata

Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake sanya hannu a dokar mafi qarancin albashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar hutun ma’aikata na kowace shekara wanda kuma ita ce aka amince da ranar Dimokaradiyya.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Sanata Ita Enang, ne ya bayyanawa wakilinmu hakan yau Litinin.

Sanata Ita, ya ce an soke hutun ranar ma’aikata da aka saba yi a kowace ranar 29 ga watan Mayu, inda aka mayae gurbin hutun zuwa 12 ga watan Yuni.