15 ga Janairu ta zama ranar tunawa da shugabannin farko na Najeriya
15 Ga Janairu, 2014 ta zama ranar Tunawa da shugabannin Najeriya na farko, kuma mafi inganci da kasar ta taba samu. A ranar 15-1-1966 ne aka yi wa Firayinministan Najeriya na farko kisan gilla. A Ranar ne kuma aka kashe wasu shugabannin kasar nan da dama, wadanda suka hada da tsohon Ministan Kudi Oktie Oboh, […]
15 Ga Janairu, 2014 ta zama ranar Tunawa da shugabannin Najeriya na farko, kuma mafi inganci da kasar ta taba samu. A ranar 15-1-1966 ne aka yi wa Firayinministan Najeriya na farko kisan gilla. A Ranar ne kuma aka kashe wasu shugabannin kasar nan da dama, wadanda suka hada da tsohon Ministan Kudi Oktie Oboh, Firimiyan Yamma Samuel Ladoke Akintola da Firimiyan Arewa, Sa Ahamdu Bello Sardauna da Manjo Kur Muhammad da Manjo Zakari Maimalari da sauransu.
Kuma masana sun yadda cewa,wannan rana ce mafi muni a tarihin Najeriya. Domin wadannan ne suna shugabannin kirki, wadanda suka dora kasar bisa turbar mutunci, amma son rai yasa wasu kidahuman sojoji kashe su.
Babu wata hujja isassa da zai sa a kashe Tafawa Balewa.To yai masu? kuma mike gare shi? Wadanda sukai juyin mulkin, sun fake da cin hanci da rashawa.To Don Allah mu kalli abin da kyau, yau wa zai nuna mana gidajen da Tafawa balewa ya mallaka? Ina son a nuna mani kamfanonin Sardauna a Najeriya, ko a wata kasa, ko kuwa a nuna mini kadarorin Cif Akintola.To kun ga ke nan karya ake, an dai kashe su ne saboda wata manufa, amma ba wai don cin hanci ba.
Saboda sadaukarwa ta wadannan shugabanni ya zama dole mu tuna da su, to sai dai akwai makiya Najeriya, makiya talakawan Najeriya, wadanda ba sa kaunar a tuna da wadannan mutane, wannan yasa irin wadannan miyagun mutane kan yi kamfen din batanci akan su, ko kuma su rika nuna rauninsu a matsayinsu na ‘yan Adam..Da ma babu wanda ya ce sun cika 10.Tara ne, kuma sun yi kura-kurai a matsayinsu na ‘yan Adam, kazalika ba za a rasa rauni tare da su ba.To sai dai sun fi wadannan barayin azzaluman marasa imani wadanda dukiya da tara kaddarori ne ke gabansu.
Idan muka nazarci Firayiminista Tafawa balewa, za mu ga gwarzon shugaba, mai kamun kai da kaskantar da kai. Wannan yasa yakan fadi cewa magana ma, bai dace a yi ta ba, sai lokacin da ta dace. A lokacin da yake wannan gugar zana,’yan jam’iyyar AG ta su Awowolo,’yan baranda irin su Bode Thomas da Dauda Adegbenro suna ta sakin maganganu na rashin tunani a Majalisar Tarayya da ke Legas.
Ko suturar Tafawa balewa kawai, wato farar babbar Riga,’yar ciki da rawani,sun isa abin misali ga wadannan munafukan shugabannin masu ware miliyoyin kudi a kasafin kudi da sunan kudin kayan da za su saka.
Tafawa balewa ba shi da komai, haka ya bar duniya, kuma ga shi ya huta, domin ga shi kowa yana yabon shi, saboda ba duniyar ce a gabansa ba.Ya sha fadin cewa “idan ba ku bukata ta, to ku bani sa’a in tattara kayana in tafi in ba ku wuri” Ya yi wannan magana ce a lokacin ana tsananin dambarwar siyasar Jamhuriya ta farko, musamman yadda Jam’iyyar Adawa ta AG ke ta haddasa fitintinu a Yammacin Najeriya. Amma yau a Najeriya wane Gwamna ko Shugaban kasa ne zai ce idan mutane ba su son shi, su ba shi ‘yan awowi ya kwashe kayansa ya koma kauyensu? Mutanen da ke ma kokarin yin tazarce ko ta halin kaka, neman mulki ko ta halin kaka.
Lallai ‘yan Najeriya mun yi rashin adalan shugabanni masu kima da martaba a idon duniya. Lokacin Sa Abubakar Tafawa balewa, Najeriya ma ta fi kima da daraja hatta a tsakanin kasashen Afirka.Tafawa balewa ya shata manufofin hulda da kasashen ketare masu ma’ana, wadanda suka fi bai wa kasashen Afirka muhimmanci. Mutum ne mai basirar iya magana, wanda har ta kai ana yi masa kirari da mai makogwaron zinari. Ba Shugabannin yanzu ba makaryata.
Yanzu aiki na gaban talakawan Najeriya, su nemo wanda zai maye gurbin Sa Abubakar Tafawa balewa, in kuma mun kiya, sai ayi ta yaudararmu a banza kawai.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka, 08165270879.