2015: A bar ‘yan Nijeriya su zabi shugabannin da suke so -Archibishop Kaigama
Archibishop na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop-bishop na darikar katolika a Nijeriya Archibishop Ignatius Kaigama, ya bukaci a bar al’ummar Nijeriya su zabi shugabannin da suke so wadanda za su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki a zabubbukan shekarar 2015 masu zuwa. Archibishop Kaigama ya yi wannan kiran ne a […]

Archibishop na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop-bishop na darikar katolika a Nijeriya Archibishop Ignatius Kaigama, ya bukaci a bar al’ummar Nijeriya su zabi shugabannin da suke so wadanda za su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki a zabubbukan shekarar 2015 masu zuwa.
Archibishop Kaigama ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.
Ya ce ta hanyar barin ‘yan Nijeriya su zabi shugabannin da suka dace ne za a samu shugabanni masu tsoran Allah da kaunar al’ummar Nijeriya.
Ya kara da cewa, ‘’muna son zaman lafiya da cigaba a Nijeriya, muna son a kori talauci da dukkan abubuwan da suke ci mana tuwo a kwarya a Nijeriya. Don haka muna son a barmu mu zabi shugabannin da suka dace a wadannan zabubbuka. Kada a tilasta wa ‘yan Nijeriya shugabannin da ba sa so, yin haka ba damakoradiya ba ne. Mu guji siyasar danniya da murdiya, domin irin wannan siyasa ba za ta kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a Nijeriya.’’ inji shi.
Archibishop Kaigama ya ci gaba da bayanin cewa, ‘’abin takaici ne ace duk da arzikin da muke da shi a Nijeriya, a kullum muna fama da yaje-yajen aikin ma’aikatan asibiti da malaman makarantu, ga hanyoyinmu sun lalace, babu ruwan sha, babu wutar lantarki. Sannan kuma a kullum yunwa da rashin tsaro suna kashe mutane a Nijeriya, amma ana ganin ‘yan siyasa suna ta bushasha da kudade.’’
Ya ce ya kamata duk shugabannin da za a zaba a wadannan zabubbuka su lura da wannan hali da ake ciki a Nijeriya.
Da ya juna kan bukukuwan kirsimitin da ake gudanarwa kuwa, Archibishop Kaigama ya ce lokacin kirsimeti lokaci ne na nuna kauna da soyayya da zumunci a tsakanin al’ummar kirista da sauran al’umma baki daya ba tare da nuna bambancin addini ko na kabila ba. Don haka ya yi kira ga al’ummar Nijeriya su yi amfanin da wannan lokaci na kirsimeti wajen nuna kauna da soyayya da zumunci tare da mantawa da abubuwan da suka faru a baya, su zauna lafiya da junansu.