2015: Amurka za ta taimaka wa Najeriya
kasar Amurka ta ce za ta taimaka wa Najeriya wajen ganin an gudanar sahihin zabe da zai gudana cikin lumana. Mataimakin Shugaban kasar Amurk Joe Biden ne ya bayar da tabbacin a wata tattaunawa da ya yi ta waya da Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da kuma dan takarar jam’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari […]
kasar Amurka ta ce za ta taimaka wa Najeriya wajen ganin an gudanar sahihin zabe da zai gudana cikin lumana.
Mataimakin Shugaban kasar Amurk Joe Biden ne ya bayar da tabbacin a wata tattaunawa da ya yi ta waya da Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da kuma dan takarar jam’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari shekaranjiya Laraba.
Mista Biden ya jinjinawa Shugaba Jonathan da Janar Buharin bisa rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi a watan Janairun bana domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben ba tare da tashin hankali ba.
Sai dai mataimakin shugaban kasar Amurkan ya kara da nuna damuwarsa dangane da tashin hankali da aka samu a kasar a lokutan kamfe, inda ya kara tunatar da ‘yan takarar bukatar da ke akwai ta yin “siyasa ba da gaba ba.”
Daga karshe, Mista Biden ya ce kasar Amurka tana maraba da sahihin zabe wanda kuma babu tashin hankali a cikinsa, sannan Amurkar za ta ci gaba da kasancewa tare da Najeriyar a kowane irin yanayi.