2015: Ba ni da dan takara – TY danjuma
Tsohon Ministan Tsaro Janar Theophilus Yakubu danjuma ya ce ba ya da dan takara kuma ba zai nema wa Shugaba Goodluck Jonathan ko wani dan takarar Shugaban kasa goyon baya a zaben 2015 ba. Janar T. Y. danjuma ya bayyana haka ne lokacin da manema labarai na fadar Shugaban kasa suka tambaye shi bayan ya […]
Tsohon Ministan Tsaro Janar Theophilus Yakubu danjuma ya ce ba ya da dan takara kuma ba zai nema wa Shugaba Goodluck Jonathan ko wani dan takarar Shugaban kasa goyon baya a zaben 2015 ba.
Janar T. Y. danjuma ya bayyana haka ne lokacin da manema labarai na fadar Shugaban kasa suka tambaye shi bayan ya yi ganawar sirri da Jonathan a shekaranjiya Laraba, inda ya ce shi ba dan wata jam’iyyar siyasa ba ce.
Tsohon Minstan Tsaron ya isa gidan Shugaban kasar ne da misalin karfe 9:30 inda ya fice da karfe 9:42 na safe.
danjuma wanda ke tare da Jonathan da mukarrabansa ke tare da shi,ya shaida wa manema labaran cewa yanzu ya dawo daga kasar waje kuma ya ziyarci Shugaban kasa ne don ya san yadda abubuwa suke tafiya a Najeriya.
Ya ce abin da suka tattauna da Shugaban sirri ne, inda ya bukaci ’yan jaridar da kada su yi shaci-fadi a kai. Da aka tambye shi abin da suka tattauna da Shugaban kasar sai ya ce: “Sirri ne. Kada ku yi shaci-fadi. Na ziyarci Shugaban kasa ne don sanin yadda al’amura suke tafiya. Ina kasar waje, kwanan nan na dawo.”
Game da ko zai nema wa wani goyon baya, musamman Jonathan a zabe mai zuwa, danjuma ya ce: “Ba zan nema ba. Ba na cikin kowace Jam’iyyar siyasa. Shugaban, Shugaban Najeriya ne.”
Tsohon Ministan bai kuma ce zai nema wa wani dan takara goyon baya a zaben ba.