2015: Fadakarwa ga al’ummar Jihar Katsina
Ya zama wajibi a gare ni kuma na ga ya kamata in jawo hankalin ’yan uwanmu talakawa, wadanda masu mulki suke ci da gumin su; a kan wani abu da ya taba faruwa a 2011 kuma yake shirin sake faruwa a 2015.Sanata Yakubu Lado danmarke, mutumin da al’ummar Jihar Katsina suka hakkake cewa shi ne […]
Ya zama wajibi a gare ni kuma na ga ya kamata in jawo hankalin ’yan uwanmu talakawa, wadanda masu mulki suke ci da gumin su; a kan wani abu da ya taba faruwa a 2011 kuma yake shirin sake faruwa a 2015.
Sanata Yakubu Lado danmarke, mutumin da al’ummar Jihar Katsina suka hakkake cewa shi ne dan takarar da zai iya kayar da Gwamna Ibrahim Shehu Shema a kan mulki a zaben 2011. Shi ne wanda ya yi farin jinin da babu wani dan takara da ya yi kamarsa, shi ne ke da goyon bayan dimbin matasa da dattawa.
Saboda soyayyar al’ummar Katsina ga Yakubu, sai da ta kai ga matasa na nuna fushinsu a kan kamun da ’yan sanda suka yi masa bisa tuhumarsa da hannu a wani zargin eho da kuma jifar tawagar Gwamna Shema.
Abin takaici, duk da dimbin magoyansa, sai ya juya musu baya, ya koma wajen gwamnati. Da yawan wadanda suka zabe shi, sun yi ne don ganin an samu ci gaban Jihar Katsina. Da yawan magoya bayansa a wancan karon sun ce sun daina zabe saboda abin da ya yi musu, wasu ma rantsuwa suka yi.
Sanin kowa ne cewa manyan jam’iyyu a Najeriya guda 2 ne, APC da PDP amma abin mamaki, da rana tsaka sai ga danmarke dauke da wata jam’iyya mai cocila, PDM. Ni na dauka zai gane kuransa na baya, ya zo mu hada kai mu ceto al’ummar Jihar Katsina da ma Najeriya gaba daya, ashe shi har yanzu ba ta canza zane ba.
A yanzu jama’a na zargin cewa ya dauko tallar jam’iyyar ne don ya nemi kudi da ita, ta hanyar raba kan al’umma da ’yan takara. Amma da yawan al’umma sun ki amincewa da haka saboda idan bakin maciji ya sare ka, idan ka ga bakin tsumma dole ka razana.
Wata bakar yaudara, sai aka sa wasu matasa suka rika shelanta wa mata cewar za a ba su tallafi, amma sai wadda take da katin jam’iyyar PDM. Shi ya sa mata suke cika wurin yin rijistar domin samun katin.
Abin da nake son tunatar da al’ummar Jihar Katsina shi ne, su yi hattara da irin wadannan ’yan siyasa, wannan cocilar da ya dauko yana son kashe idanuwan mutane, don ya zambace su karo na biyu. Sannan ina kira ga ’yan takara su hada kansu, su fitar mana da kwakkwara ba mayaudari ba kuma ba wanda za a yi amfani da shi a yaudari jama’a ba; don gudun komawa ’yar gidan jiya.
dandattijo Bayan NEPA Malumfashi (07039018940)