2015: Goyon bayan Gwamnonin PDP ga Jonathan bai ba ni mamaki ba – Sheikh dahiru Bauchi
Sheikh dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya a tattaunawarsu da wakilinmu ya bayyana yadda ya ji lokacin da gwamnonn PDP suka nuna goyon bayansu ga Jonathan don ya sake tsayawa takara kuma ya bukaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike kan kama jirgin Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya […]
Sheikh dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya a tattaunawarsu da wakilinmu ya bayyana yadda ya ji lokacin da gwamnonn PDP suka nuna goyon bayansu ga Jonathan don ya sake tsayawa takara kuma ya bukaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike kan kama jirgin Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a yunkurin safarar makamai a Afirka ta Kudu:
Me za ka ce kan gwamnonin da suka mara wa Jonathan baya ya ci gaba da mulki a 2015?
Gwamnonin da suka ce suna goyon bayan Shugaba Jonathan ya ci gaba da mulki a zaben 2015 ba su da wani iko sai abin da Shugaban kasa ya ba su umarni. Don haka ban yi mamaki ba da suka bayyana maitarsu a fili, amma ga su ga ’yan Najeriya Allah Ya kai mu shekara ta 2015. Maganar ’yan siyasa daban, maganar Shugaban kasa daban, maganar Allah daban. Saboda haka muna jiran lokacin da Allah zai kawo mana canji a Najeriya.
To idan Shugaba Jonathan ya nace sai ya sake tsayawa takara me kake ji zai biyo baya?
Allah ne kawai ya san makomar Najeriya nan da 2015 amma tabbas ba ma jin dadin abubuwan da ke faruwa a gwamnatin Jonathan saboda haka ya kamata gwamnati ta yi gyara tsakaninta da Allah, ana hallaka Musulmin Najeriya ya kamata a daina kashe mana mutane haka.
Me ya sa kake danganta kungiyar Izala da Boko Haram?
Bari na fada maka maganar gaskiya wanda babu wani dan jarida da muka taba yin wannan hira da shi, akwai wani masallaci da aka gina a garin Damaturu da ke Jihar Yobe inda aka shafe sama da shekaru masallacin na hannunmu, kwatsam wata rana sai ’yan Izala suka hana yin wazifa a masallacin. Tun daga lokacin Allah Ya jefa mu cikin halin da muke ciki a yau na tashe-tashen hankula. Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam yana daya daga cikin wadanda suka yi ta kai ruwa rana da Muhammad Yusuf wanda ya kafa Boko Haram. Akwai lokacin da muka hadu da shi a fadar Sarkin Kazaure, a gabana Sarkin Kazaure ya yi masa tambaya sai ya ce ba zai amsa ba, tunda babban malaminmu Sheikh dahiru Bauchi na wajen. Wannan magana da Ja’afar ya yi ya nuna cewa tabbas yana da ilimi da sanin ya kamata, sannan yana mutunta dattawa sabanin yadda sauran ’yan Izala ke kallonmu. Har zuwa lokacin da wasu marasa imani suka yi masa kisan gilla, duk inda ya gan ni yana mutunta ni. Sannan ya dauke ni a matsayin cikakken Musulmi dan Tijjaniya. Bayan haka akwai wani lokaci da muka sake haduwa da shi sai ya ce min Shehi tunda kake ka taba jin ina wa’azi ina kafirta ’yan Tijjaniya? Sai na ce a gaskiya ban taba ji kana wa’azi kana zagin mutane ba. Soboda haka a cewar Ja’afar wajibi ne duk wani malamin da yake bukatar hadin kan Musulmin Najeriya ya rika mutunta dattawa da masu farin gemu. Sheikh Ja’afar har zuwa lokacin mutuwarsa ba dan Izala ba ne, amma yana wa’azi a karkashin kungiyar Izala kuma ina yi masa addu’a Allah Ya gafarta masa da sauran Musulmin duniya. Daga nesa idan dan Izala ya ga Sheikh dahiru Bauchi sai ya ce ga mushiriki can, da zarar na matso kusa sai ka ji yana cewa Allah Ya gafarta Malam. Wadanda suka koma suna cewa karatun boko haram ne, aikin gwamnati haram ne har suka dauki makamai suna yakar gwamnatin da sojoji da ’yan sanda, daga kungiyar Izala suka fito domin babu wani dan Tijjaniya da ke sukar aikin gwamnati da karatun boko. Da ma akwai wasu daga cikin Kiristocin Najeriya da suke jin haushi Musulmi suna ta karatun boko a ciki da wajen kasar nan.
Me za ka ce game da jirgin da aka kama na shugaban kungiyar CAN dauke da makuden kudi da aka ce za a sayo makamai ne?
Tabbas a makon jiya kafafen watsa labarai sun ce an kama jirgin Shugaban kungiyar CAN Pasto Ayo Oritsejifor dauke da makudan kudi a kasar Afirka ta Kudu inda ake zargin za a sayo makamai ne da kudin.
Tun daga lokacin da aka kama jirgin ’yan Najeriya suna ta bayyana ra’ayoyinsu ta kafafen watsa labarai cewa ya kamata gwamnati ta yi bincike na gaskiya game da batun. Lokacin da na samu labarin na rubuta takarda ga Barista Solomon Dalung daya daga cikin ’ya’yan kungiyar Dattawan Arewa, saboda na san cewa mutum ne da yake da adalci na fadar gaskiya komai dacinsa. Har zuwa yau babu wani mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka na zahiri game da jirgin. Kuma a halin yanzu ya kamata al’umma su gane cewa sojojin Najeriya sun kasu gida biyu akwai sojojin gwamnati akwai sojojin da ke yakar Musulmi da Arewa. Sojojin gwamnati ba su da makamai masu inganci amma wadancan sojoji suna da makamai masu inganci kirar zamani. Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon lalacewar gwamnati, amma duk da haka za mu ci gaba da yin addu’o’i na musamman ga masu neman wargaza kasar, Allah Ya ci gaba da tona musu asiri. An kashe mana dimbin mutane a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da sauran jihohi da ake mana kisan dauki-dai-dai, amma duk da haka Gwamnatin Tarayya ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka ban ga amfanin wannan gwamnati ba. Tunda kake ka taba ganin wani malamin addinin Musulunci a Najeriya da jirgi mallakarsa? Saboda haka gwamnati ta yi bincike na gaskiya ko mu ci gaba da matsa mata lamba. Dama wasu majiyoyi sun tsegunta mana cewa kafin zaben shekara ta 2015 za a ci gaba da kashe Musulmi da kona musu gidaje da sunan yaki da kungiyar Boko Haram da ke tada kayar baya. Motocin ’ya’yan kungiyar Boko Haram da motocin sojojin Najeriya suna kama da juna, ya kamata gwamnati ta fada mana gaskiyar abubuwan da ke faruwa a wadannan jihohi da aka hallaka dimbin Musulmi.
A karshe mene ne sakonka ga ’yan Najeriya?
Babban sakona ga ’yan Najeriya shi ne ya kamata kowa ya gyara tsakaninsa da Allah mu tuba daga aikata miyagun laifuffuka sai Allah Ya magance mana matsalolin da muke fuskanta.
Kowa ya ga abubuwan da suke faruwa a jihohin Arewa maso Gabas na hare-hare da kashe-kashe, kusan kullum sai ka ji an kashe sama da mutum goma a Najeriya. Muna rokon Allah Ya ba mu zaman lafiya a jihohinmu da Najeriya baki daya.