2015: Jonathan da Sambo za su kashe Naira biliyan 4 a kan abinci da tafiye-tafiye

A kasafin kudin da Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta mika wa ’yan majalisar tarayya a zauren majalisarsu a ranar Larabar makon jiya, kasafin ya bayyana Shugaba Goodluck Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo za su kashe Naira biliyan 4 a kan abinci da kuma wajen tafiye-tafiye.Fadar shugaban kasa tana da kason Naira biliyan 26 da miliyan […]

2015: Jonathan da Sambo za su kashe Naira biliyan 4 a kan abinci da tafiye-tafiye
2015: Jonathan da Sambo za su kashe Naira biliyan 4 a kan abinci da tafiye-tafiye

A kasafin kudin da Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta mika wa ’yan majalisar tarayya a zauren majalisarsu a ranar Larabar makon jiya, kasafin ya bayyana Shugaba Goodluck Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo za su kashe Naira biliyan 4 a kan abinci da kuma wajen tafiye-tafiye.
Fadar shugaban kasa tana da kason Naira biliyan 26 da miliyan 600 a cikin kasafin kudin, kodayake za a iya samun sauyi tun da kasafin kudin yana zauren majalisa don a yi zama a kansa.
A cikin kasafin kudin Jonathan zai kashe Naira biliyan1.9 wajen tafiye-tafiye da sauran abubuwan da suka shafi sufuri, inda sauran ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya za su kashe Naira biliyan 1.3 a kan abin da ya shafi tafiye-tafiye a cikin gida, inda za a kashe Naira miliyan 621 a kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo zai kashe Naira miliyan 42.4 wajen tafiye-tafiye, inda sauran ma’aikatan da ke ofishinsa za su kashe Naira biliyan 19.6 wajen tafiye-tafiyen a cikin gida. Za su kuma kashe Naira biliyan 10.7 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Za a kashe Naira miliyan 12 wajen tafiye-tafiyen cikin gida da bada horo a bangaren sufuri.
 Shugaba Jonathan zai kuma kashe Naira miliyan N517.8 a kan abubuwan da za su iya tasowa, zai karbi Naira miliyan 456 wajen gabatar da jawabai da kuma zaman taro. Zai kashe Naira miliyan 60.8 wajen tallace-tallace. Sambo zai kashe Naira 117 wajen abubuwan da za su iya tasowa, zai karbi Naira miliyan 15 wajen zaman taro da kuma Naira 35 wajen tallace-tallace.
Bayanin kasafin kudin da Aminiya ta samu ne ta gano shugaban kasa da mataimakinsa za su kashe Naira biliyan 1.2 wajen kayan abinci da na kicin.
An bayyana za su yi amfani da Naira miliyan 310 wajen sayan magunguna da kayayyakin da suka shafi dakin binciken lafiya. Za a kashe Naira miliyan 13.5 wajen sayen abincin namun dajin da ke gidan Namun Daji a gidan gwamnatin tarayya.