2015: Jonathan ya fara kamun kafa a wurin sarakuna

A wani yunkuri da ake jin na kamun kafa ne domin tsayawa takara a zaben shekarar 2015  mai zuwa, Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya fara ziyartar manyan sarakuna a sassan kasar nan, sai dai kuma Shugaban kasar ya ce ziyarar ba ta da alaka da siyasa ko batun neman tsayawa takara a badi.A karshen […]

2015: Jonathan ya fara kamun kafa a wurin sarakuna

A wani yunkuri da ake jin na kamun kafa ne domin tsayawa takara a zaben shekarar 2015  mai zuwa, Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya fara ziyartar manyan sarakuna a sassan kasar nan, sai dai kuma Shugaban kasar ya ce ziyarar ba ta da alaka da siyasa ko batun neman tsayawa takara a badi.
A karshen makon jiya ne Shugaba Jonathan ya kai ziyara ga Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Alaafin na Oyo Oba Lamidi Oyiwola Adeyemi na Uku da kuma Ooni na Ife Oba Okunade Sijiwade.
Daga baya wata majiya ta ce ya kai iri wannan ziyara ga Oba na Legas da kuma Akran na Badagry duk a Jihar Legas.
Kawo yanzu mukarraban Shugaban kasar ba su bayyana hakikanin batutuwan da ya tattauna da sarakunan ba, lamarin da ya sa jama’a da dama ke danganta ziyarar da siyasa, inda suke zargi Shugaba Jonathan da neman goyon bayan masarautun kasar don sake tsayawa takara.
A Kano Shugaba Jonathan ya ce ya je ne domin duba lafiyar Sarkin tare dag ode wa masarautar kan kokarinta na tabbatar da zaman lafiya jihar. Ya ce, “Na dade ina son in gan ka tun dawowarka jinya daga kasar waje. Kuma ina farin cikin iske ka cikin koshin lafiya. Ya shaida wa Sarkin cewa yana shirye ya karbi shawara daga sarakuna inda ya bukaci Sarkin ya ci gaba da shiryarwa da kuma karfafa shugabannin siyasa.
Sarkin ya gode wa Shugaban kasa kan ziyarar inda ya bukace shi ya rungumi daukacin ’yan Najeriya a yayin gudanar da mulkinsa.
“Ka rike kowa da adalci, wannan kasa ce daya kuma kai ne shugabanta. Ka tafiyar da harkokin kasar nan ta hanyar da kowa zai yi alfaharin shi dan Najeriya ne,” inji Sarkin Kano.
Ya kuma bukaci Shugaban kasar ya kare zage dantse wajen magance matsalolin tsaro da suke addabar kasar nan.
Wadanda suka rufa wa Shugaban kasar baya yayin ziyarar sun hada da mashawarcinsa kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya tarbe su.
Daga baya Shugaba Jonathan ya zarce zuwa birnin Oyo a Jihar Oyo inda ya gana da Alaafin of Oyo, Oba Lamidi Olyiwola Adeyemi III, kafin ya isa birnin Ile-Ife da ke Jihar Osun domin ganawa da Ooni na Ife Oba Okunade Sijuwade.