2015: Lokacin da sauran shiyyoyin Bauchi za su fito da Gwamna
Tarihin Arewacin Najeriya bai zai kammala ba sai an hada da irin gwagwarmayar da wasu masu jihadi da kuma malamai suka yi kamar su , Malam Ibrahim Zaki na masarautar Katagum da Gwani Mukhtar na masarautar Misau da kuma Malam Muhammadu Wabi na masarautar Jama’are, wadanda suka kafa yankin da a yau ake kira Arewacin […]
Tarihin Arewacin Najeriya bai zai kammala ba sai an hada da irin gwagwarmayar da wasu masu jihadi da kuma malamai suka yi kamar su , Malam Ibrahim Zaki na masarautar Katagum da Gwani Mukhtar na masarautar Misau da kuma Malam Muhammadu Wabi na masarautar Jama’are, wadanda suka kafa yankin da a yau ake kira Arewacin Bauchi da kuma wani bangare na shiyyar Bauchi ta Tsakiya sai Malam Yakubu wanda ya kafa tasa masarautar a Bauchi ta Kudu da wani bangare na Bauchi ta Tsakiya, wadannan mujahidai sun bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban wannan yanki da kuma Jihar Bauchi, musamman ta hanyar dabi’ar nan ta cuda-ni-in cude ka ko taimakekeniya a tsakaninsu.
Kuma irin wannan dabi’a ce ta ci gaba har zuwa lokacin da aka samu wata yerjejeniya a 1998 a tsakanin mazabun sanata na Arewaci da Tsakiya da Kudancin Bauchi. Wannan yarjejeniya ta kullu ne lokacin da aka unkari zaben 1999 wanda ya kawo tsohon Gwamna Ahmadu Adamu Mu’azu kan kujerar mulkin jihar.
Abubuwan da aka yanke shawara a kai kansu a wancan lokaci sun hada da rabon manyan mukamai a jihar da sauransu. Kuma a karkashin wannan fahimta ce aka mika wa Sakataren Gwamnatin Jihar a zamanin Gwamna Mu’azu, Alhaji Muhammed Nadada Umar (daga masarautar Misau a mazabar Bauchi ta Tsakiya) tikitin takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2007. Sai dai kuma Malam Isa Yuguda (daga Bauchi ta Kudu) wanda ya tsaya takara a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP ya samu nasara a kansa a zaben.
Damuwata ita ce yadda yarjejeniyar ta ba da dama ga dabi’ar nan ta wanda ya samu nasara ya kwashe komai. Wannan ya sa Bauchi ta Kudu ke rike da manyan ofisoshi mafiya girma. Duk gefen da aka duba wannan tsari da ake kai yana danne sauran shiyyoyin jihar.
Domin haka a ka’idar nan ta adalci, al’ummar shiyyoyin Bauchi ta Arewa da Bauchi ta Tsakiya suna da yakinin cewa yanzu lokacinsu ne su fito dag Gwamnan Jihar. A daidai lokacin da zaben badi ke kara kusantowa, gwagwarmayar neman kujerar ta fara kankama, musamman yadda ake ruwan posta-posta a kan tituna da falwayoyi da shatale-shatale da gine-ginen gwamnati da na jama’a.
Akwai zargin cewa wani minista yana amfani da wasu ’yan siyasa daga shiyyoyin dan Majalisar Dattawa na Bauchi ta Arewa da Bauchi ta Kudu domin neman goyon bayan jama’ar shiyyar ga bukatarsa. Sai dai abin bakin ciki, ministan yana amfani ne da ’yan siyasar da ba su da tagomashi a kokarinsa na cimma bukatar zaman Gwamna a zaben badi. Bai dace ba a ce ministan ya sanya mutumin da ya gaza lokacin da yake sanata daga mazabar Bauchi ta Tsakiya domin cimma wannan buri nasa.
Duk dan siyasar da yake son cimma nasara akwai bukatar ya yi amfani da dan siyasar da yake da karbuwa, sananne, mai alkibla da manufa kuma jama’a suke sonsa. Don haka ina fata ministan zai gane kuskurensa ya yi gyara tun kafin lokaci ya kure.
Fatata ’yan siyasa sun koyi darasi daga yin butulci ga wadanda suka taimake su, ko jam’iyyar da ta kai su gadon mulki. Irin wannan hali ne ya sanya Jam’iyyar PDP ta fadi a zaben shekarar 2007. Gaskiyar magana ita ce, ’yan siyasar da ba su da tagomashi kan sadaukar da kansu wajen yin aiki ga duk wanda zai rika ba su kudi suna gararin gabansu. Ga irinsu komai ta fanjama fanjam, tunda ba su da komai.
Manufar samun mutunci a siyasa ita ce ta jagoranci kyautata halin mutane domin samun ingancin aiki; amma a Jihar Bauchi sabanin haka ke samuwa. An yi watsi da batun mutunci a fagen siyasa ta yadda ’yan ma’abba suka tashi tsaye ido a rufe don karbe mulki.
A dimokuradiyya ta hakika a wannan zamani, akwai akidar karfafa rungumar juna da adalci da ba kowa hakkinsa da kuma daidaito, da ke da dabi’ar fahimtar juna a tsakanin jama’a masu bambancin manufa. Wannan ne ya sa ta zamana tsarin gwamnati da aka fi amfani da shi a kasashen da suka ci gaba da kasashe masu wayewa a duk duniya a yau.
Muna son fadi karara cewa ba mu da wani mugun kulli kan burin ministan, amma halin da ake ciki inda aka bar wani yanki ya mamaye harkokin jihar abu ne da bai dace ba, kuma wajibi ne a sanya aya ga haka. Mun zama ’yan rakiya a harkokin siyasar Jihar Bauchi, a tsawon lokaci. Mutane na nuna mu a matsayin wasu mutane da ba mu da karfin hali, mutanen da ba su yarda da kansu ba, kuma mutanen da ba za su iya fitowa ko gabatar da wanda zai iya tsayawa takarar Gwamna ba. Muna ganin hakan a matsayin cin zarafi kuma cin fuska gare mu.
Mun yi imani tsarin karba-karba a shi ne kawai hanya ta kawo zaman lafiya da fahimtar juna da mutunta juna da ’yan uwantaka da kawo ci gaba da bunkasar jiharmu da al’ummarta. Wannan shi ne lokacin da ya dace mu karfafa tsarin karba-karba a wannan jiha.
Mohammed Ameer, Bakin Kasuwa, Azare, Jihar Bauchi.