2015: Maku ya fara haduwa da miki

Tsohon Ministan Watsa Labarai da ke neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar PDP Mista Labaran Maku ya fara haduwa da miki, bayan da fusatattun ma’aikatan ma’aikatarsa suka tayar da bore a wurin bikin mika harkar ma’aikatar. Ma’aikatan sun yi bore ne domin nuna bacin ransu kan yadda aka kasa biyansu wasu alawus-alawus […]

2015: Maku ya fara haduwa da miki
2015: Maku ya fara haduwa da miki

Tsohon Ministan Watsa Labarai da ke neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar PDP Mista Labaran Maku ya fara haduwa da miki, bayan da fusatattun ma’aikatan ma’aikatarsa suka tayar da bore a wurin bikin mika harkar ma’aikatar.

Ma’aikatan sun yi bore ne domin nuna bacin ransu kan yadda aka kasa biyansu wasu alawus-alawus dinsu a lokacin tsohon Ministan da kuma zargin da suka yi ga Ministan da manyan jami’ansa kan almubazzarantar da kudin rage radadin karin kudin mai (SURE-P) da aka ba ma’aikatar.
Ma’aikatan a karkashin jagorancin kungiyar manyan ma’aikata ta Najeriya (Association of Senior Cibil Serbants of Nigeria) reshen Ma’aikatar Watsa Labarai ta Tarayya sun kukkule kofofin shiga ginin Radio House hedkwatar ma’aikatar na awanni, inda suka hana mutane shiga ko fita daga ginin.
Fusatattun ma’aikatan sun rika rera wakoki dauke da kwalayen da aka yi rubuce-rubucen da suka hada da: “Shin kudin SURE-P da aka bayar don aljifan wasun mutane ne?’ da “Ko ba a sake kudin kasafin Ma’aikatar Watsa Labarai na 2014 ba ne?” Sauran sun hada da “Tura ta kai bango: Shugabannin ma’aikatar ba su damu da jin dadin ma’aikata ba,” da “A sallami Babbar Sakatariya,” da sauransu.
Da yake magana da manema labarai shugaban kungiyar ma’aikatan Adam Ogwola ya ce mahukuntan ma’aikatar ba su damu da jin dadin ma’aikata ba, inda ya kawo misali da yadda ba a biyansu wasu alawus- alawus da ya ce murabus din Ministan na iya sa a kasa kwato wadannan kudade.
kungiyar ta zargi Mista Maku da rarraba wani bangare na kudin SURE-P tsakaninsa da manyan jami’an ma’aikatar ba tare da tunawa da sauran ma’aikata ba.
Mista Ogwola ya ce tun lokacin da Maku ya zama minister harkokin kula da jin dadin ma’aikata suka rika yin kasa, inda ya ce a zamaninsa ma’aikatar ba ta biyan wasu muhimman alawus-alawus ga ma’aikata.
Ya tuhumi batun kasafin ma’aikatar na bana, inda ya yi kiran a gaggauta cire Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Folashade Yemi-Esan.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa tsohon Ministan ya bayyana wa niyyarsa ta ganawa da wakilan goma-goma na ma’aikatan gidan Rediyon Najeriya da na Muryar Najeriya da na Ma’aikatar Watsa Labarai da na Hukumar Talabijin ta kasa, wajen liyafar cin abinci domin a warware matsalar da ta taso. Kakakin Maku Joseph Mutuah ya bayyana wa jaridar cewa “Ana tattaunawa kuma an warware komai.”
A makon jiya ne Minista Maku da wasu takwarorinsa shida suka yi murabus domin tsayawa takarar gwamnoni a jihohinsu.