2015: Ministoci bakwai sun yi murabus
Tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya domin ci gaban kasar nan. Janar Abubakar ya yi wannan kira ne a garin Gombe a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya da taya murna ga sabon Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar a ranar Litinin din da ta gabata.Janar Abdulsalami Abubakar, […]
Tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya domin ci gaban kasar nan.
Janar Abubakar ya yi wannan kira ne a garin Gombe a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya da taya murna ga sabon Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar a ranar Litinin din da ta gabata.
Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce muddin babu zaman lafiya a kasa babu abind a zai tafi daidai.
Game da zabubbukan da ke tafe a badi ya yi addu’ar Allah Ya sa a yi zaben lafiya kuma kasa ta ci gaba da zama lafiya har bayan zabe.
Janar Abubakar, ya ce a lokacin da marigayi Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usman Abubakar, yake jinya a kasar Ingilla suna tare, amma da Allah Ya yi masa rasuwa bai samu zuwa ya yi ta’aziya ba saboda wasu matsaloli.
Ya ce saboda alakarsa da Sarki a lokacin da yake raye hakan ya sa yake ganin ba iyalan Sarkin ne suka yi rashi ba kasa ne baki daya ne.
Da yake mayar da jawabi Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, gode wa Janar din ya yi bisa ta’aziya da taya
murna da ya yi musu inda ya ce ya san irin kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin marigayi da Janar din.
Sarkin ya ce yana fata wannan alaka da kuma aminantaka ta ci gaba kamar yadda suka yi da mahaifinsa.
Janar din ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abba Musa Rimi da wasu manyan mutane daga Minna da wasu daga cikin ’ya’yansa.