2015: Na kusa bayyana matsayina- Tambuwal

Imam dalhatu Imam shi ne mai magana da yawun Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. Aminiya ta tuntube shi kan batun taron Jam’iyyar APC a Sakkwato da aka rawaito shugaban majalisar ya halarta, inda ya ce har yanzu Tambuwal yana neman shawara, kuma nan ba dadewa ba zai bayyana matsayinsa. Ga yadda hirar ta […]

2015: Na kusa bayyana matsayina- Tambuwal

Imam dalhatu Imam shi ne mai magana da yawun Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. Aminiya ta tuntube shi kan batun taron Jam’iyyar APC a Sakkwato da aka rawaito shugaban majalisar ya halarta, inda ya ce har yanzu Tambuwal yana neman shawara, kuma nan ba dadewa ba zai bayyana matsayinsa. Ga yadda hirar ta kasance: 

Aminiya: A ranar Litinin ne aka ga Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a wurin taron Jam’iyyar APC da aka yi a Sakkwato, to Hausawa sun ce idan aka ga kare na shinshina takalmi to dauka zai yi, me ya kai shi taron APC?
Imam dalhatu: Ba taron Jam’iyyar APC ba ne, taro ne na masu ruwa da tsaki wajen neman ci gaban Jihar Sakkwato, idan aka duba wadanda suka halarci taron za a ga akwai manya-manyan mutane wadanda ba a ’yan siyasa ba ne kamar su Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji, saboda idan har dattijo kamarsa ya halarci taro kamar wannan, to ka ga taro ne da ba za a jingina shi da na jam’iyyar siyasa daya kawai ba, duk wadanda suka halarci taron sun ji taken taro ne na masu ruwa da tsaki wajen ci gaban Jihar Sakkwato. Su ne suka shirya taro, sannan suka gayyace shi, kuma ya je.
Aminiya: Wata majiya ta ce Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko ya saya wa Shugaban Majalisa fom don tsayawa takara a Jam’iyyar APC, haka ne?
Imam dalhatu: Ba ni ba ne ya kamata in amsa wannan tambayar, Gwamna ya kamata ya amsa tambayar, yanzu idan wani ya ce na yanka maka tikiti ko fom, ba kai za ka ba da amsa ba, ni da na fada ne zan ba da amsa, don haka ba ni ya dace ka yi wa wannan tambayar ba.
Aminiya: Mun tambaye ka ne saboda kana magana a madadinsa…
Imam dalhatu: Ba dai mu ya dace mu yi bayanin ba, gwamna ne zai yi cikakken bayani.
Aminiya: Amma an buga a jaridu cewa Gwamna Wamakko ya ce Tambuwal yana cikin Jam’iyyar APC tsundum?
Imam dalhatu: Ka ga wannan duk bayani ne da ya kamata Gwamna ya yi cikakken bayani a kai, ba Tambuwal ba, yanzu misali na ce kai Balarabe Ladan na APC ko wata jam’iyya, ai ka ga ba kai ya kamata a tambaya ba, ni ya kamata a tambaya, za a tambaye ni me ya sa na ce haka, yanzu dai gwamna ya fada, shi ne kuma zai yi cikakken bayani.
Aminiya: Masu magana sun ce idan ga maciji ba a nuna ja, wani zai ce karya ne, wani kuma ya ce da gaske ne, don haka ku bayyana wa mutane gaskiyar magana?
Imam dalhatu: Ba za mu ce haka ba, kai ne ka fada, ni dai ba zan iya cewa komai a kan wannan ba.
Aminiya: Yanzu ina Tambuwal ya sa gaba ne, takarar gwamna zai yi, ko ta shugaban kasa?
Imam dalhatu: A yanzu ana yi masa tambayoyi kusan guda uku, ta farko wacce jam’iyya zai yi? Sannan takarar me zai yi? Da kuma batun ina ya dosa a dangane da batun zabe mai zuwa? Ina so mutane su sani komai yana hannun Ubangiji, yanzu dai yana nan yana shawara da manya, yana shawara da jama’arsa a Sakkwato da Tambuwal da kuma mutanen Najeriya gaba daya, kuma insha Allahu yana kammalawa da kansa zai bayyana wa duniya matsayar da ya cim ma, mutum ne mai fadar ra’ayinsa, kuma duk abin Tambuwal yake son ya fada, to yana fada, saboda haka jama’a su ci gaba da hakuri har ya bayyana musu inda ya dosa.
Aminiya: Yanzu noke-noken da yake ta yi ba zai bata dangantakarsa da ’yan Jam’iyyar PDP ba, saboda za su ga kamar ba a san inda ya sa gaba ba?
Imam dalhatu: Ya gaya musu inda ya sa gaba, kuma kafin ya yi takarar dan majalisa sai da ya yi shawara da jama’a, inda suka tambaye shi me zai yi, da farko ya ce ku yi hakuri ina neman shawara a wurin jama’a, bayan ya kammala neman shawara sai ya sanar wa mutane zai yi takarar majalisar wakilai ta tarayya, haka bayan zaben shekara ta 2011, wato bayan ya je majalisa aka sake tambayarsa me zai nema a majalisa kasancewar yana daya daga cikin ’yan majalisun da suka san makamar aiki, a nan ma ya ce wa jama’a su yi hakuri, bayan ya kammala neman shawara ya ce zai nemi matsayin shugaban majalisa, inda kuma Allah Ya ba shi nasara, a yanzu ma ina so mutane su yi hakuri, insha Allahu zai fito ya bayyana matsayarsa, a yanzu da nake magana ya fada wa abokansa na jam’iyya da kannensa da kuma mu da muke tare da shi cewa yana neman shawara, kuma idan ya kammala zai yi bayani.
Aminiya: Yanzu duk shawarar da jama’a suka ba shi, da ita zai yi amfani ke nan?
Imam dalhatu: Tabbas wannan haka yake, duk wurin da jama’a suka ce ya dosa, to nan zai dosa.
Aminiya: Ko da zai kai ga barin Jam’iyyar PDP ne?
Imam dalhatu: A dai bari ya gama neman shawarar tukunna, amma dai na tabbatar maka duk abin da jama’a suka yanke, to da shi zai yi amfani.

Muna maraba da shi -APC

Alhaji Usman dan Madamin Isa shi ne mataimakin shugaban jam’iyar APC na jihar Sakkwato, ya yi wa Aminiya karin haske kan zuwan Aminu Waziri Tambuwal taron jam’iyar APC ta jihar Sakkwato.

Daga Nasiru Bello Sakkwato

Aminiya: Ya kake kallon lamarin nan na Aminu Waziri Tambuwal da ya shigo taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarku da aka gudanar a jihar nan ba tare da ya bayyana ficewarsa a jam’iyar PDP ba?
dan Madami: Wannan lamari mai sauki ne, saboda idan ka lura manyan jagororinmu sun yi bayani sun ce daman tare da su yake, idan ka lura kuma shi kamar mutum ne da ita kanta PDP ta riga ta yaye shi, ba ta da bukatarsa, don a lokacin nadin sarautarsa babu wani dan PDP na a-zo-a-gani da ya halarci bikin nadin, duk ‘yan APC ne. Don haka ita siyasa ra’ayi ce, ko mutum ya fadi ko kar ya fadi da baki, abin da ya yi a aikace shi ne ake amfani da shi, to tun da lamurran APC yana yinsu a aikace mai yiwuwa ne yana da wata hujja da ta hana shi ya furta ya bar PDP a halin yanzu, sai nan gaba.
Aminiya: Ba ka ganin jam’iyar APC a nan Jihar Sakkwato ba za ta yi sawarwari ba na tsayawa jiran wanda bai canja sheka ba, tun da ana kallon sai ya zo ne za ku san matsayar kujerar gwamna?
dan Madami:To ka san irin wannan kiyasi naku ne na ‘yan jarida, mu abin da muke gani ba jiransa ne jam’iyyar APC take yi ba, domin akwai masu neman kujerar da yawa, kuma mai girma gwamna ya sanar da mu a wurin taron da aka yi kwanan nan cewa ba shi da dan takara duk a cikinsu, ka ga ba batun shi ake jira, don lamarin jam’iyya na tafiya lami lafiya, idan ko aka ce shi ake jira to an yi kuskure.
Aminiya: Kana ganin idan ya samu tikitin jam’iyyarku kwalliya za ta biya kudin sabulu, duk da ana ganin jam’iyyar PDP za ta dauki mataki mai tsauri a kansa?
dan madami:To mai yiwuwa su dauka kuma suna iya kyale shi, amma a nan idan ya san yana da laifi to me zai sa ya fito takara a jam’iyyarmu da zai iya haddasa mana rasa kujerarmu? To idan ka ga ya fito takarar gwamna ba shi da laifi ke nan, don ba zai zo ya bata lokacinsa da lokacin mutanen jiha ba, a koma ana kuka da shi.
Aminiya: Duk da ganinsa da aka yi a taron naku daga baya ya ce ba taron siyasa ba ne, me za ka ce kan haka?
dan Madami: Ni gaskiya bai yi wannan magana da ni ba, kuma ban gani a jarida ba, babu wanda ya zo mini da wannan magana, don haka ni ba zan yanke hukunci kan wannan ba, don kowa na da damar fadin abin ya sani a kansa.
Aminiya: Ya kake ganin kwamitin da aka kafa domin fitar da ‘yan takarar da suka cancanta tsayawa neman kujerar gwamna, wanda har Aminu Waziri na cikin wadanda za a duba cancantarsu?
dan Madami: Kwamitin an sanya shi bisa ka’ida ta jam’iyya domin zaben fitar da gwani, yana iya kawo wa jam’iyya cikas. Sai dai ina bai wa wannan kwamiti shawarar da ya yi adalci, su yi zaman sirri da dukkan shugabannin kananan hukumomi 23 na mulki da na jam’iyya da kwamishinoni da shugabbanin jam’iyya na jiha da ‘yan majalisar tarayya da na jiha, domin sanin wane ne ya fi cancantar a zaba, duk wanda ya fi yawan jama’a sai a mara masa baya, idan aka yi haka zai yi wuya a ce wannan ba zabin Sakkwatawa ba ne, kuma zai samar da maslaha sosai, don kowa ya san an ba shi hakkinsa, an fitar da zabin al’umma.

Ya sauka lafiya -PDP

Alhaji Ibrahim Milgoma shi ne shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato, shi ma Aminiya ta tattauna da shi kan halartar taron APC da Tambuwal ya yi.

Aminiya: Me za ka ce kan batun taron APC da Aminu Tambuwal ya yi?
Milgoma: To ka san maganar APC ba maganarmu ba ce, tasu ce daban, mu ‘yan PDP ne, kuma ina ganina Aminu Waziri ya dade da barin PDP, don tun hawana wannan kujera ban gan shi a taronmu ba, don haka ba abin mamaki ba ne idan an gan shi a taron APC, dama tare da mutanen yake, mutanen PDP sun dauki Aminu dan APC ne, taron kasa da na jiha ba ka ganinsa, don haka mu ba mu ma san halin da yake ciki ba, ballantana a ce ya shanya taronmu, don ba don shi ake taron ba, kuma a matsayina na ciyaman bai taba nema na ba, duk dan PDP ko zai neme ni don harkar jam’iyya, ba mu huldar jam’iyya da shi, ka ko ga ba dan PDP ba ne, da ya neme mu.
Aminiya: Kuna ganin idan ya fitar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyarku ba zai girgiza ku ba tare da kawo muku cikas ko koma-baya ba?
Milgoma: Ko daya ba zai girgiza mu ba, don mun san ba dan PDP ba ne, don bai halarci zaben shugabanin jam’iyya ba, kuma duk dan PDP ya halarci taron, fiye da shekara daya ko biyu mutanen Jihar Sakkwato ba su gan shi cikin harkokin PDP ba, don haka babu dalilin da zai sanya idan ya fice daga jam’iyyar ya bata mata suna, kila dai ya yi PDP ne tare da Wamakko lokacin da mu ba mu cikinta, amma lokacin da muka shigo ba mu same shi a cikinta ba, kuma bai aiko mana cewa shi dan PDP ba ne, hasali ma dai bai karbi katin jam’iyya a wurinmu ba wanda aka sabunta kwanakin baya, kai ba shi da katin jam’iyyar PDP, to dan jam’iyya ba shi da katin jam’iyya to dan jam’iyya ne?
Aminiya: Ana zargin ku ne ba ku gayyatarsa taronku don haka ne ba ya halarta don bai san da shi ba.
Milgoma:Wata daban, ni ba ni cewa mun kira shi, amma tun da muka ga bai halarci na kasa a matsayinsa na jigo a can, don haka muka shafa wa kanmu ruwa kada mu wuce makadi da rawa, saboda shi jigo ne a jam’iyyar PDP, shugaban kasa ya zo nan jihar sau biyu, amma ba tare da shi ba, kuma babu wani dalili da aka sanar mana da ya hana shi zuwa, don ko ba komai gidansa ne ya zo, ka ga ya dace su zo tare, amma saboda ya bar jam’iyyar bai zo ba, zan kara da babbar murya babu wata dangantaka tsakaninmu da shi ta siyasa.
Aminiya: To idan ya canja ra’ayin bai furta ficewa a jam’iyyarku ba har ya nemi tsayawa takarar wata kujera za ku amince masa?
Milgoma: Ita PDP kofarta a bude take, duk wanda ya zo a shirye muke mu yi tafiya tare, ko dan APC ne, balle shi da kaurace wa lamurran jam’iyya, don mu ba mu kyamar kowa. Sarautar da aka nada shi ma bai gayyace mu ba da mun halarta, don haka dai ya bar mu.