2015: Sanatocin PDP sun tada kayar baya

A karo na biyu cikin makon nan, sanatocin da suka fito daga Jam’iyyar PDP, sun jawo Majalisar Dattawa ta kasa zama a shekaranjiya Laraba, kan yunkurin kwace kujerunsu da gwamnonin jihohi ke yi.  A ranar Talata an zauna na minti 30 ne a majalisar bayan dawowa daga hutun mako daya, sakamakon abin da suka kira […]

2015: Sanatocin PDP sun tada kayar baya
2015: Sanatocin PDP sun tada kayar baya

A karo na biyu cikin makon nan, sanatocin da suka fito daga Jam’iyyar PDP, sun jawo Majalisar Dattawa ta kasa zama a shekaranjiya Laraba, kan yunkurin kwace kujerunsu da gwamnonin jihohi ke yi. 

A ranar Talata an zauna na minti 30 ne a majalisar bayan dawowa daga hutun mako daya, sakamakon abin da suka kira “kasa” cika alkawarin Shugaban kasa na ba su tikitin dawowa kai-tsaye.
Da majlisar ta sake dawowa shekaranjiya, sai ta jingine daukacin batutuwan da aka jero don tattaunawa kuma ta dage zamanta zuwa ranar Talata mai zuwa.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark ya bayyana wa abokan aikinsa cewa majalisar ba za ta zauna ba, sakamakon ganawar shugabannin PDP a majalisar za su yi. Nan take sai shugaban masu rinjaye Sanata bictor Ndoma-Egba na PDP daga Kuros Riba ya gabatar da bukatar dage zaman majalisar zuwa wata rana, inda shugaban marasa rinjaye Sanata Ahmed Sani na APC daga Zamfara ya goyi bayansa.
Bayan taron Sanata Ndoma-Egba ya shaida wa manema labarai cewa, “Ina da tabbacin kuna sane cewa shugabannin PDP a majalisa sun gana a ranakun Talata da Laraba kan wasu muhimman batutuwa da suke shafar dimokuradiyya a Najeriya da suka taso daga zaben unguwanni na Asabar da ta gabata. Akwai bukatar a warware batutuwan cikin gaggawa a tsakanin masu ruwa da tsaki a PDP domin amfanin dimokuradiyyarmu.”
Yunkurin wasu gwamnoni da ke zangon karshe na wa’adinsu na maye gurabun sanatocin da suka fito daga jihohinsu ne ya jawo tsaiko ga zaman majalisar dattawan. An ce sanatocin sun samu tabbaci daga Shugaba Jonathan cewa za a ba su tikitin komawa kan kujerunsu.
Aminiya ta tuno lokacin da aka kafa sabuwar PDP wadda ta hade da APC, an yi wa sanatocin alkawarin bar musu kujerunsu idan suka ci gaba da zama a PDP. Wannan ne ya sa daga cikin sanatocin PDP 22 da aka sa ran su koma APC, 11 ne kawai suka koma.
A watan Satumban bara ne aka cimma yarjejeniyar bar musu kujerunsu lokacin da Shugaban Kwamitin Dattawa da Shugaban Jam’iyyar na lokacin Alhaji Bamanga Tukur suka gana da sanatocin suka roke su kan kada su bar jam’iyyar zuwa ta adawa.
An ga sanatocin sun fito fuskokinsu a murtuke bayan dage zaman cikin minti 30 da fara shi.
Daga nana ne shugabannin PDP suka shiga taron gaggawa kan lamarin, inda suka sha alwashin ci gaba da kaurace wa zaman majalisar har sai Shugaban kasa ya tabbatar musu da tikitin takara kai-tsaye.
daya daga cikin barazanar da sanatocin PDP suke yi shi ne na goyon bayan Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Tambuwal wanda a makon jiya ya koma Jam’iyyarb APC.
Aminiya ta samu bayani cewa sanatocin PDP sun gana da Shugaba Jonathan da misalign karfe 10 na dare, amma ba ta samu bayanin abin da suka tattauna ba har zuwa hada wannan rahoto.
dage zaman majalisar bai yi wa sanatocin APC dadi ba, inda suka ce bai kamata sanatocin PDP su rika fifita bukatunsu na siyasa kan bukatun kasa ba.
Sanata Babafemi Ojudu na APC daga Ekiti wanda ya yi magana da manema labarai kan batun ya ce, sanatocin PDP suna haduwa da sakamakon mulkin Gadara da jam’iyyarsu take yi ne. Ya ce don me za su rika kuka.”Idan muka samu yadda muke so, za mu zo gobe mu zauna, ba abu ne na bukatar kai ba, kamata ya yi ya zaman a jama’a,” inji shi.
Ya ce “Yanzu da zalunci ya shafe su ne suka fara fada. Mun shekara biyu da rabi muna ganin rashin adakci. Mun yi kokarin fada, amma suka hana mu…. Yanzu da suka ga da yawansu ba a maraba da su a gida ne suka gane sun mayar da kansu bayi ga bangaren zartarwa.”
Sanatan ya ce, sanatocin PDP sun mayar da kansu ‘bayi’ ga bangaren zartarwa inda suka ci gaba da dakile ’yan adawa a majalisar don kare Gwamnatin Tarayya a duk lokacin da suke nuna gazawar bangaren zartarwa, “wannan ne sakamakon aikinsu na shekaru,” inji shi.
Ya ce za su kira taron shugabanninsu don tattauna wannan batu, kuma suna sa ran za su kira su taro. “Bai kamata su zo su dage zaman majalisa kamar haka kawai ba. Wasunmu sun zo daga mazabunsu da ke nesa don mu zauna a wannan mako, amma an hana mu zama.”

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi