2015: Surukin Awolowo ne zai mara wa Buhari baya
A yayin da shekarar zabe ta 2015 ke kwankwasa kofa kuma ya rage watanni biyu a gudanar da babban zaben Shugaban kasa da sauransu, ta tabbata dai za a fafata gumurzu ne tsakanin manyan jam’iyyun APC da kuma PDP; musamman ma bayan fitar da ’yan takararsu da mataimakansu da suka yi a kwanakin nan.A jam’iyyar […]

A yayin da shekarar zabe ta 2015 ke kwankwasa kofa kuma ya rage watanni biyu a gudanar da babban zaben Shugaban kasa da sauransu, ta tabbata dai za a fafata gumurzu ne tsakanin manyan jam’iyyun APC da kuma PDP; musamman ma bayan fitar da ’yan takararsu da mataimakansu da suka yi a kwanakin nan.
A jam’iyyar APC, wacce ta tsayar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin dan takara, ta kuma tsayar da Mista Yemi Osinbanjo a matsayin wanda zai mara masa baya a matsayin dan takarar Mataimakin Shuagban kasa. Bincike dai ya tabbatar da cewa Mista Yemi, wanda masanin shari’a ne, suruki ne kuma ga marigayi Cif Obafemi Awolowo, domin yana auren jikanyarsa.
A ranar Larabar makon jiya ce dai Jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta a Abuja, inda ta tabbatar da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takararta da zai nemi maimaita shugabancin Najeriya a babban zaben da ake sa ran gudanarwa a watan Fabrairu mai zuwa, kuma ya bayyana cewa Namadi Sambo ne zai mara masa baya a wannan fafatawar da za a yi.
Wani abin da ya dauki hankalin ’yan Najeriya, a yayin babban taron na PDP shi ne, babu wani dan takara da ya kalubalanci Shugaba Jonathan, shi kadai ne jam’iyyar ta ba damar tsayawa, abin da ya bambanta da taro irinsa da aka gudanar kafin zaben 2011, inda tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Uwargida Sarah Jibril suka fafata da shi a zaben fitar da gwani na jam’iyyar.
Ita kuwa Jam’iyyar APC, ta fitar da tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Janar Muhammadu Buhari (ritaya) ne, a babban taron jam’iyyar da ya gudana a Legas a ranakun Laraba da Alhamis na makon jiya. Ba kamar Jam’iyyar PDP ba, a Jam’iyyar APC sai da aka fafata takara tsakanin mutane biyar da suka hada da shi kansa Muhammadu Buhari, Alhaji Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma Sam Nda-Isaiah.
Wani muhimmin al’amari kuma da ya zama jigo a gaban ’yan takarar shugabancin kasar shi ne batun zaben Mataimakin Shugaban kasa. Duk da a watannin baya an yi ta baza rade-radin cewa Shugaba Jonathan ba zai shiga zabe tare da mataimakinsa na yanzu, Alhaji Namadi Sambo ba, amma a ranar Alhamis ta makon jiya sai ya ayyana shi a matsayin wanda zai mara masa baya a zaben.
Kafin Shugaba Jonathan ya rufe bakin tsanya, a can baya an yi ta hasashen cewa zai canja Namadi Sambo da daya daga cikin gwamnonin Arewa. Sunayen Gwamnan Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema da na Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da na Jihar Bauchi, Alhaji Isa Yuguda ne aka yi ta bazawa a batun, kafin daga bisani dai aka tabbatar da sunan Alhaji Namadi Sambo.
A Jam’iyyar APC kuwa, al’amarin zaben mataimakin dan takarar Shugaban kasa ya zafafa, inda al’amarin ya zama tamkar cin kwan makauniya. Al’amarin ya sha bamban da takarar 2011, inda Janar Buhari da kansa ya zabi wanda ya mara masa baya, ba tare da an kai ruwa rana ba. A wancan lokacin, ya zabi Pastor Tunde Bakare ne a matsayin mataimakinsa. Sai dai a wannan karon, al’amarin ya dauki sabon salo, inda aka maida hankali kan addini da yankin da dan takarar zai fito.
Tun da farko, a hirar da ya yi da Sashen Hausa na BBC a makon jiya, Janar Buhari ya bayyana cewa shi ba zai zabi mataimakinsa da kansa, kamar yadda ya saba ba, zai mika al’amarin ga uwar jam’iyya domin zabar mutumin da ya dace.
Kamar yadda ya ce, yanayi ya canja, yanzu an shigo da al’amarin addini da bangaranci a cikin siyasa, don haka dole ne a yi la’akari da haka wajen zaben wanda zai mara masa baya.
Tun a cikin daren ranar Lahadin da ta gabata ce shugabannin jam’iyyar da mukarrabanta, musamman gwamnoninta suka hadu da nufin fidda mutum daya da zai mara wa Janar Muhammadu Buhari baya a takarar shugabancin kasa amma hakarsu ba ta cin ma ruwa ba har sai ranar Larabar da ta gabata suka cin ma matsaya a kan Farfesa Yemi Osinbanjo.
Da farkon tattaunawar zabin mataimakin, sunayen Mista Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Legas Babatunde Fashola da Gwamnan Ribas Rotimi Amaechi da Gwamnan Edo Adams Ashiomole da kuma shi Osinbanjon ne aka gabatar da nufin daukar guda daya cikinsu.
Shi dai Farfesa Yemi Osinbanjo, dan shekara 55 da biyar ne kuma babban lauya (SAN) ne wanda sau biyu ya taba rike mukamin Kwamishinan Shari’a na Jihar Legas. Haka kuma babban mai wa’azin Kisista ne a Majami’ar Redeemed Christian Church of God. Ganin cewa an zabe shi, Jam’iyyar APC ta cika ka’ida ke nan, tun da ta tura sunansa ga Hukumar Zabe (INEC) cikin lokaci, domin kuwa kamar yadda dokar zabe ta 2010 ta nuna, jiya Alhamis ce rana ta karshe da jam’iyyu za su iya tura sunan wanda suka zaba a matsayin mataimakin dan takara.