2015: Wajibi ne Jonathan ya janye daga takara – Rabaran Okotie
Shugaban cocin Household of God, Rabaran Chris Okotie, ya ce halin da Shugaba Goodluck Jonathan ya samu kansa da kalubalen da ke gabansa a matsayin dan takara daidai ne da na Shugaban Amurka na 36, Lyndon Johnson, inda ya ce bambancin da ke tsakaninsu kawai shi ne Shugaban na Najeriya ya ki ya bi abin […]
Shugaban cocin Household of God, Rabaran Chris Okotie, ya ce halin da Shugaba Goodluck Jonathan ya samu kansa da kalubalen da ke gabansa a matsayin dan takara daidai ne da na Shugaban Amurka na 36, Lyndon Johnson, inda ya ce bambancin da ke tsakaninsu kawai shi ne Shugaban na Najeriya ya ki ya bi abin da ya kira hanyar girma da mutunci.
A wata wasika da ya rubuta a shafinsa na Facebook, limamin Kiristan ya ce Najeriya a yanzu tana fuskantar kalubale mai yawa irin wadanda Shugaba Johnson wanda ya karbi mulki lokacin da aka kashe Shugaba John Kennedy, da suka sanya ya janye daga niyyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu.
Rabaran Okotie ya nuna mamaki kan abin da zai sa a lokacin da rashin tsaro ke karuwa tattalin arziki ke koma baya, amma Jonathan ya ki ya bi hanyar da mutumin da suka yi kamanceciniya da shi a fannoni da dama ya bi.
“Johnson da Jonathan duk mataimakan shugabannin kasa ne da suka gaji masu gidansu lokacin da suka mutu a gadon mulki, kuma suka sake tsayawa takara suka ci zabe a kashin kansu. Shugabannin biyu sun jagoranci kasashensu a lokaci na bala’in siyasa; misali Johnson ya fuskanci yakin Biyatenam, shi kuma Jonathan yana fama da hare-haren Boko Haram da sauran munanan abubuwa. Wannan ne irin kamanceceniyar da suka yi.”
“Shugaba Johnson ya ba duniya mamaki a lokacin da ake tsakiyar zaben fidda-gwani domin zaben shugaban kasar na 1968, inda kwatsam ya janye daga takarar saboda korafe-korafen da ake yi kansa na gaza magance yakin Biyatenam da kuma tashe-tashen hankulan nuna bambancin launin fata. Hakan da ya yi, ya sa an rika yaba masa, saboda martabar da daukar wannan mataki da ya yi ta jawo masa, kuma an sanya shi cikin dattawan Amurka. Ya zabi zaman lafiyar kasarsa a kan son zuciyarsa duk da zakin da ke cikin mulki,” inji shi.
Rabaran Okotie ya nuna damuwa kan yadda duk da rikice-rikicen da kasar nan ke fama da su, Jonathan ya tankwara shugabannin Jam’iyyar PDP sun tsayar da shi a matsayin dan takara guda daya, alhali ya dace ya bi hanyar girma ya janye domin alfanun kasar nan.
“Yana shugabancin kasa ce da ta yi muguwar rarrabuwa, kyamar juna kan dalilin addini ya kekketa ta, ga tsabagen cin hanci a tsakanin jami’an gwamnati, kuma an yi mugun gazawa wajen magance hare-haren ’yan Boko Haram. Kuma a yayin da wannan muguwar gazawa ya kamata ta sa ya ajiye burinsa na neman shugabanci kamar Johnson, sai Jonathan ya yi dabarun da suka sa ya samu damar tsayawa takara ba hamayya a zaben 2015.”
“Shi da jam’iyyarsa ta PDP sun kasa gane cewa, idan ba za ka iya magance matsala ba, to ba makawa kai kanka bangare ne na matsalar. Wannan ne ya sa Shugaba Johnson bai nemi a sake zabensa ba. Shugaban na Amurka ya san cewa bambancin da ke tsakanin mutunci da rashin mutunci, sai ya zabi hanyar mutunci,” inji Okotie.
Limamin Kiristan ya ce akwai bambanci a tsakanin ’yancin da tsarin mulki ya bayar da kuma batun mutunci, inda ya ce ’yanci kan zama banza ko bala’i idan aka rasa mutunci. Ya ce Shugaba Jonathan yana jagorancin wasu sojoji ne da galibinsu “masu tsoron yaki ne,” lamarin da ya sa suke gudu daga fagen fama kungiya-kungiya, hakan ya tilasta su fifita batun sulhu fiye da mayakan Boko Haram.
Sannan ga “abin bakin ciki na makomar ’yan matan Chibok da karuwar cin hanci da almundahana da tabarbarewar tattalin arziki, a cewar Okotie, zabin da ya fi ga Shugaban kasa shi ne irin matakin da Johnson ya dauka shekara 46 da suka gabata.
Ya ce, amma maimakon haka, Jonathan ya fi mayar da hankali dabarun siyasa da za su ba shi damar samun nasara a badi. “daya daga cikin abin ban takaici, shi ne yadda Shugaba Jonathan ke bin hanyoyin da suka saba wa dimokuradiyya wajen ganin an sake ba shi dama a zabe mai zuwa. Tun kafin Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta dage kamfe, PDP ta kirkiro wasu kungiyoyin magoya Jonathan a sassan kasar nan. Kuma fiye da kowane Shugaban kasa, Jonathan ya yi amfani da kujerarsa domin amfanin kashin kansa, ya yi amfani da jami’an tsaro da dukiyar kasa a duk inda ya ga dama; misali ta hanyar lalata Majalisar Gwamnoni da ke yi masa barazana kan sake zabensa, ko cire gwamnonin da ba su yi masa biyayya ta hanyar shirya tsige su. Shugaban kasa ya yi amfani da dabaru da yawa don cimma manufa guda: share hanyar sake zabensa a 2015! Idan wannan ita ce ake nufi da dimkoradiyya, to lallai muna cikin babbar matsala,” inji Okotie.
Wasikar ta Okotie dai ta jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, a yayin da wasu suka nuna rashin jin dadinsu cewa Shugaba Jonathan bai damu da halin da kasar nan take ciki ba, kamar yadda Rabaran Okotie ya fada, wasu kuwa sun soki rabaran din ne da cewa shi ma bai nuna shugabancin da ya dace.
Wasu ma sun yi zargin cewa wai ’yan bokon Arewa ne suke amfani da Boko Haram domin juya akalar ’yan Arewa marasa ilimi, kamar yadda wata mai suna Maureen Ifeanyichukwu ta fadi a martaninta.
Shi kuwa Dabid Akpakpan cewa ya yi ganin yadda jama’a suke son Jonathan a yanzu fiye da shekara hudu da suka gabata, wata shaida ce cewa mafi yawan ’yan Najeriya ba su da ra’ayi irin na Okotie.