2019: Babu shakka Buhari ne mafita
Babu shakka Shugaba Muhammad Buhari shi ne mutumin da ya fi cancanta mu sake goya wa baya a wannan karon domin ba shi damar cika burinsa na alheri da ya sanya a gaba domin aza kasarmu a kan tudun mun tsira a zaben 2019. Kada mu manta fa Shugaba Muhammadu Buhari shi ne Shugaban da […]
Babu shakka Shugaba Muhammad Buhari shi ne mutumin da ya fi cancanta mu sake goya wa baya a wannan karon domin ba shi damar cika burinsa na alheri da ya sanya a gaba domin aza kasarmu a kan tudun mun tsira a zaben 2019.
Kada mu manta fa Shugaba Muhammadu Buhari shi ne Shugaban da har yanzu babu wata hukumar da ta taba zargi ko tuhumarsa da cin hanci ko rashawa, saboda ba shi ne a gabansa ba.
Babban abin da ke gaban Shugaba Muhammadu Buhari bai wuce yaya za a yi a samu tulin ci gaba a bangaren farfado da tattalin arzikin kasa da samar da tsaro a kasa, tare da samar wa matasa ayyukan yi ba.
Ya kamata ’yan Najeriya mu yi karatun ta-natsu tare da cire duk wani ra’ayi a bangaren siyasa mara tasiri. Mu dawo mu rungumi hanyar da za ta kai mu samun ingattacen jagoranci a kasarmu mai albarka.
Muna ganin irin yadda wannan dattijo ke fadi-tashi ba dare ba rana wajen tafiye-tafiye da balaguro zuwa kasashe daban-daban a sassan duniya domin ganin kasarmu ta samu gagarumin ci gaba.
A idonmu muke ganin yadda yake tilasta wa hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICIPC da sauransu wajen ganin sun kamo barayin kasarmu domin kwatar abin da suka sata na daga dukiyar kasa.
Akwai kudirori masu yawa na alheri da ya sanya a gaba, to idan ba mu ba shi damar komawa ba yana da wuya a iya aiwatar da abubuwan da ya tsara.
Maganar fatara da yunwa da rashin aikin yi tsakanin mutane, wannan ya samo asali ne sakamakon durkusar da tattalin arzikin kasarmu shekara 4 zuwa 4 da suka wuce.
Idan muka duba da kyau a yanzu babu abin da ya sa a gaba illa ganin ya magance wadannan matsaloli.
A karshe ina jan hankalin ’yan uwana ’yan Najeriya cewa tsalle daya dai ake yi a fada rijiya, amma sai a yi bubu ba a fito ba.
Allah Ya zaba mana shugabanni na kwarai masu kishin kasa ba masu kishin aljihunsu ba. Amin
Nura Sani Rijau
08108291641
Whatspp: 08026664213