2019: Buhari zai samu kuri’u kadan a Arewa – Shekarau
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce Shugaba Buhari ba zai samu kuri’u masu yawa a zaben 2019 a yankunan Arewa, ba kamar yadda ya samu a zaben 2015. Shekarau ya ce, hasashen da aka yi game da yawan kuri’un da dan takara na jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar wanda shi ma haifaffen […]
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce Shugaba Buhari ba zai samu kuri’u masu yawa a zaben 2019 a yankunan Arewa, ba kamar yadda ya samu a zaben 2015.
Shekarau ya ce, hasashen da aka yi game da yawan kuri’un da dan takara na jam’iyyar adawa PDP Atiku Abubakar wanda shi ma haifaffen Arewa ne, wanda hakan zai rage yawan kuri’un da Shugaba Buhari ya samu.
Shekarau ya kara da cewa zaben 2019 ba zai zama mai sauki kamar na 2015 ba.