2019: Buhari zai samu kuri’u miliyan 5 a Kano- Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana aniyyarsa na samawa Shugaba Buhari kuri’un jihar miliyan 5 a zaben shugaban kasa na 2019. Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne jiya a Kano yayin gangamin  siyasa da kuma karban tsohon Gwamnan jihar Ibrahim Shekarau da ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya dawo jam’iyya APC da […]

2019: Buhari zai samu kuri’u miliyan 5 a Kano- Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana aniyyarsa na samawa Shugaba Buhari kuri’un jihar miliyan 5 a zaben shugaban kasa na 2019.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne jiya a Kano yayin gangamin  siyasa da kuma karban tsohon Gwamnan jihar Ibrahim Shekarau da ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya dawo jam’iyya APC da dai sauran ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka zuwa APC.

Gwamnan ya kara da cewa, jam’iyyar APC kadai ce a Kano da tafi kowa ce jam’iyya mambobi kuma zata yi iya bakin kokarinta don lashe zaben Gwamnan jihar da na Shugaban Kasa, na majalisar wakilan tarayya da na dokokin jihar.