2019: Ina fata Buhari zai yi koyi da Jonathan – Sule Lamido

Ba ka da bakin magana – dansadau Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi koyi da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan idan ya fadi a zabe wajen amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa da za a yi a shekarar 2019, inda ya ce alamu sun nuna cewa […]

2019: Ina fata Buhari zai yi koyi da Jonathan – Sule Lamido

Ba ka da bakin magana – dansadau

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi koyi da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan idan ya fadi a zabe wajen amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa da za a yi a shekarar 2019, inda ya ce alamu sun nuna cewa PDP za ta kwace mulki.

Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Tattaunawa ta Shekara-Shekara na jaridar Daily Trust karo na 15 da aka gudanar jiya Alhamis a Abuja. 

Alhaji Sule Lamido yana cikin manya masu jawabi uku da jaridar ta gayyata a taron na bana mai taken: “Najeriya da kalubalen Shekarar 2019.” 

Ya ce “Kowa a nan shaida ne cewa an karanta mana a cikin jawabin Shugaban kasa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha ya wakilta, inda ya ce Goodluck Jonathan ya nuna dattaku tare da martaba bukatar kasa a maimakon nasa na kashin kai wajen amincewa da shan kaye. Don haka muna fatan Shugaba Buhari zai yi koyi da Jonathan a 2019 idan ya fadi zabe.” 

Alhaji Sule Lamido ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari da kuma jagoran Jam’iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu kan gaza shawo kan matsalar karancin man fetur da take addabar al’ummar kasar nan tsawon lokaci. Sai ya yi shagube da cewa, “Na tabbata ma motar Cif Tinubu tana can a layin neman mai a Legas, dalilin da ya hana shi halartar wannan taro, wanda yana daya daga cikin manyan baki masu jawabi, amma rashin man fetur ya hana shi zuwa,” inji Lamido.

Tsohon Gwamnan, wanda yake ci gaba da fuskantar shari’a kan cin hanci da rashawa, ya kalubalnci manufofin gwamnatin Buhari wadanda ya ce ba su da ingancin da za su taimaki talakan kasar nan. Sannan ya yi gugar zana ga Shugaba Buhari, cewa yana da masaniya game da kudaden da ake zargin Janar Abacha ya sace ya boye a kasashen waje, inda ya ce kusan tare suka yi mulkin kasar a lokacin. “A kwanan nan fa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya sanya hannu a kan yarjejeniyar dawo da kudaden da Abacha ya sace, amma wani ya ce bai saci komai ba, wanne za mu dauka ke nan?” inji shi.

A jawabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukan ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa su mai da hankali kan kalaman da za su karfafa zaman lafiya da gudanar da tarurruka cikin lumana.

Shugaban kasar wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha ya wakilta, ya kuma bukaci ’yan siyasa su mutunta dokokin zabe kuma su nisanci haddasa rigingimu a tsakanin jama’a. Ya ce akwai bukatar dukan jam’iyyun siyasa su marbata dokokin kasar nan yayin aiwatar da al’amuransu.

Ya ce “A daidai lokacin da muke fuskantar zabubbuka masu zuwa, wajibi ne a kanmu baki daya mu tabbatar da cewa mun gina ingantaccen ginshikin kyakkyawar manufar dimokuradiyya a kasar nan saboda al’ummarmu baki daya.”

Ya jijina wa kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya kan shirya wannan muhimmin taro mai taken yadda za magance matsalolin zabubbukan shekarar 2019, wanda hakan abu ne da zai yi tasiri a siyasar kasar nan. 

A jawabin jagoran Jam’iyyar APC, Cif Bola Tinubu wanda ke daya ne daga cikin masu jawabi a taron da Mista Wale Edun ya wakilta, ya ce wannan lokaci ba lokaci ne na adawa da yakin neman neman zabe ba, saboda lokacin bai yi ba, “Yanzu abin da ke gabanmu shi ne yadda za mu fuskancin matsalolin da suke tafe a zabubbuka masu zuwa a matsayinmu na kasa daya al’umma daya.”

Da yake tsokaci a wurin taron Sanata Sa’idu Muhammad dansadau ya ce tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ba ya da bakin magana, domin a lokacin da aka fafata takarar Shugaban kasa a farkon wannan zubin siyasar Lamidon ya goya wa marigayi Cif Aled Ekwueme baya ne maimakon Cif Olusegun Obasanjo.

Sanata dansadau yana mayar da martani ni ga Lamido kan cewar da ya yi Jam’iyyar PDP a dunkule take har ta fito da toshon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo inda ya yi takara ya cinye zaben Shugaban kasa. 

Sanata dansadau ya ce, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Abba Musa Rimi ya neme shi ya kai shi wurin tsohon Shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar don ya taimaka wa Alhaji Umaru Shinkafi saboda shi yake so ya gaje shi a 1999. Amma daga baya sojoji suke ce a fito da Cif Obasanjo daga kurkuru domin shi suke so ya zama musu Shugaban kasa. 

“Wasu daga cikin abubuwan da abokina Sule Lamido ya fada game da Jam’iyyar PDP ba gaskiya ba ne. A 1999, Sule Lamido bai goyi bayan Obasanjo ba, Lamido Aled Ekwueme ya goya wa baya. Alhaji Sule Lamido kada ka manta ka goyi bayan Cif Aled Ekwueme ne a taron jam’iyyar da aka yi a Jos. Daga baya ne bayan Cif Obasanjo ya kada sauran ’yan takara sai ka koma kana bin bayan Obasanjo,” inji dansadau.

Ya kara da cewa amfanin ilimi shi ne a koyar da yara manyan gobe yadda za su amfani al’umma, “Ana tunawa da shugabannin farko ne saboda yadda suka yi aikin kwarai, kuma hakan ya samo asali ne saboda su ma malamai ne.Yawancin shugabannin yanzu ba su san muhimmanci ilimi ba, wannan ne ya sa muke fama da rashin shugabanci na kwarai,” inji shi. 

Tun farko a jawabiin Shugaban Kamfanin Media Trust Ltd, mai buga jaridun Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf ya ce, “An kafa jaridar Daily Trust ce a Kaduna a 1998. Kuma ana shirye-shiryen cikarta shekara ashirin da kafuwa a bana. Ya ce, an fara taron tattaunawa na shekara-shakara na jaridar ne domin nemo bakin zare kan yadda za a magance cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki da siyasa. 

Ya ce samun lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari abin mamaki ne, inda bayan ya warke tare da ci gaba da tafiyar da kasar nan, aka fara kiraye-kirayen ya sake tsayawa takara a zaben 2019. “Kafin dawowarsa daga jinya har wadansu sun fito da burin neman yin takara, amma da ya dawo sai suka boye. Muna fatan mu ci gaba da ba da gudunmawa wajen gina kasa,” inji shi. 

A jawabin Shugaban Taron kuma tsohon Ministan Shari’a, Yarima Bola Ajibola ya yi godiya ne kan bude ofishi da madaba’ar Daily Trust a Legas, “Mu mutanen Kudu muna murna kwarai domin mun dauki jaridar a matsayin mai bunkasa da fatan za ta ci gaba da aiki tukuru” inji shi. 

Ya bukaci a daina yi wa doka karan-tsaye domin a gina kasa mai bin doka da oda. “Ina son a sauya dokar da ta ce duk wanda za a iya nadawa a matsayin Ministan Shari’a sai ya shekara goma yana aiki, ina son a mayar da dokar sai wanda ya samu mukamin Babban Lauya a Najeriya (SAN). Kuma ya dace Ministan Shari’a da kwamishinonin sharia’u na jihohi su dage wajen tabbatar da an ba mai hakki, hakkinsa, kuma an darajta doka sannan a inganta aikin shari’a yadda ya kamata,” inji shi.

A jawabin fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Najeriya (Nollywood) kuma ’yar siyasa, Misis Kate Henshaw ta bukaci matasan Najeriya ne su fito a dama da su a harkokin mulki da tattalin arziki, inda ta ce, Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shekarunsa 39, na Belgium shekara 38, na Estoniya 38, na Tunisia 40, Kim Jun Un na Koriya t Kudu yana da shekara 30, sannan matsahiya banessa ta kasar San Marino tana da shekaru 29. “Ya kamata matasa su dage domin su gaji shugabannnin da suka kwato mana ’yanci domin matasa ne makomar kasar nan kuma kashin baya ga ci gabanta a nan gaba,” inji ta.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wurin taron, tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega cewa ya yi, “Ya kamata siyasa ta zama ana amfani ne da gaskiya da mutunci da rikon amana ba kabilanci da bangaranci ko addini ba.”