2019: kungiya ta yi wa Atiku alkawarin kuri’u miliyan 10

Wata kungiya mai suna Grassroots Network 4 Atiku (GNA) dake goyon bayan takarar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya 2019, ta yi masa alkawarin kuri’u miliyan 10. Shugaban kungiyar na kasa Barista Isa Mohammed ne ya bayyana hakan yau Litinin a Bauchi. Muhammad ya ce, kungiyar ta yi gangami wayar da […]

2019: kungiya ta yi wa Atiku alkawarin kuri’u miliyan 10

Wata kungiya mai suna Grassroots Network 4 Atiku (GNA) dake goyon bayan takarar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya 2019, ta yi masa alkawarin kuri’u miliyan 10.

Shugaban kungiyar na kasa Barista Isa Mohammed ne ya bayyana hakan yau Litinin a Bauchi.

Muhammad ya ce, kungiyar ta yi gangami wayar da kan jama’an dake da katin zabe akan marawa Atiku baya a zaben takarar shugaban kasa na 2019.

Shugaban kungiyar ya ce, a yanzu haka sun gana  da sama da ‘yan Najeriya miliyan uku kuma sun yi alkawarin zaben Atiku a matsayin shugaban Najeriya 2019.