2019: Ni ba munafuka ba ce – A’isha Alhassan
Daga Hamza Idris da Musa Abdullahi Krishi da Salihu Makera Ministar Harkokin Mata Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta ce za ta sauka daga mukaminta na Minista idan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce zai tsaya takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2019, saboda ita ba munafuka ba ce, kowa ya san Atiku ne […]

Daga Hamza Idris da Musa Abdullahi Krishi da Salihu Makera
Ministar Harkokin Mata Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta ce za ta sauka daga mukaminta na Minista idan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce zai tsaya takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2019, saboda ita ba munafuka ba ce, kowa ya san Atiku ne ubangidanta na siyasa.
Hajiya Jummai Alhassan ta bayyana haka ne a hirarta da sashin Hausa na rediyon BBC a shekaranjiya Laraba, inda ta ce ko Buhari ba zai yarda da ita ba, idan a yau ta ce babu ruwanta da Atiku.
“Mai girma Atiku ya kasance ubangidana tun kafin in shiga siyasa. Bayan na shiga siyasa ya ci gaba da kasancewa ubangidana. Ka san kowa yana da dalilinsa na dangantaka na siyasa. Na biyu Baba Buhari bai shaida mana cewa yana son tsayawa takara a shekarar 2019 ba,” inji ta.
Ta kara da cewa: “Ina tabbatar maka idan Baba Buhari ya shaida mana zai sake neman takara na rantse da Allah zan je gare shi, in shaida masa cewa, ‘Baba na gode maka kan damar da ka ba ni in yi aiki a karkashinka a matsayin Minista. Amma Baba kamar yadda ka sani, Atiku shi ne ubangidana.’ Wannan idan (Atiku) ya ce zai tsaya takara ne, amma har zuwa yanzu da muke magana (Atiku) bai shaida mana zai tsaya takarar ba.”
Minsitar ta ce, za ta sauka daga mukaminta na Minista idan Atiku ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takara, saboda zai zamo “munafunci” idan ta ci gaba da zama Minista domin biyayyarta har yanzu tana ga tsohon Mataimakin Shugaban kasa, kasancewarsa ubangidanta. “Muna fata (Atiku) zai tsaya takara a 2019, wannan ne ya sa na fadi haka. Amma har yanzu bai bayyana haka da kansa ba. Idan ya bayyana zan yi abin da na ce. Idan Atiku ya fito takara kuma na ci gaba da zama a gwamnatin Baba Buhari a lokacin, to na zamo munafuka. Kuma ba a san ni da munafunci da rashin godiya da cin amana ba,” inji ta.
Ta ce, “A yau idan na ce babu ruwana da Atiku, ko Baba Buhari da kansa zai yi shakka a kaina. Zai ce ni butulu ce, kuma ni ba irin haka nake ba.”
Da aka tambaye ta cewa ba gaggawa ba ce a fara kamfe din 2019 yanzu ba, sai Jummai Alhassan ta ce, ba kamfe take yi wa Atiku a wannan lokaci ba. “Wannan abu na fada ne lokacin da muka kai masa (Atiku) ziyarar Barka da Sallah. Shin a gabansa ne zan ce zan yi kamfe? Batun kamfe bai taso ba. Ko ni mutane suna zuwa suna cewa in fito takara kuma ina gaya musu lokaci bai yi ba, yanzu lokaci ne na yi wa jama’a aiki,” inji Ministar.
Ta ce: “Wannan aikin masu adawa da ni ne. Suna cewa a kore ni daga Minista. Tun farko ban yi tsammanin zama Minista ba. Allah ne Ya ba ni, kuma a yau idan aka ce in tafi, Allah ne Ya kawo haka. Akwai abin da aka kaddara min, kuma na yi imani duk abin da ya faru da ni haka Ubangiji Ya kaddara.”
Ta kuma ce, Buhari ba zai kore ta saboda wannan batu ba. “Shin sun dauka Buhari mahaukaci ne kamarsu? Suna ta tuttura abubuwa ta wayoyin hannu ta yadda in Baba ya gan su zai sauke ni. Ba zai sauke ni daga Minista ba saboda wannan batu, sai dai in na aikata wani babban laifi. Kuma ina yin aikina na Minista gwargwadon ikona. Kuma ina kare gwamnatin Jam’iyyar apc, jam’iyyata. Baba ne jagorana kuma shugaban kasata. Ina girmama shi kuma zan ci gaba da girmama shi a matsayinsa na mutumin kirki kuma mutum mai gaskiya da rikon amana. Don haka masu cewa a kore ni za su sha kunya. kuma koda an sauke ni lokaci ne ya yi ba wani abu ba. Ban nemi mukamin ba tun farko, Allah ne Ya ba ni.”
Shi kuwa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadi a shekaranjiya Laraba cewa gwamnatin Muhammadu Buhari wadda ya ce ya taimaka wajen kafuwarta a shekarar 2015 ta jingine shi a gefe.
korafin na Atiku ya zo ne kwana guda bayan daya daga cikin ministocin Buhari ta ce za ta yi murabus daga mukaminta idan Atiku ya bayyana cewa zai tsaya takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
A wata hirar da aka watsa a sashin Hausa na Muryar Amurka (bOA) a safiyar shekaranjiya Laraba, Atiku ya ce an jingine shi a gefe duk da cewa ya yi amfani da sanayya da matsayi da dukiyarsa wajen kawar da Jam’iyyar PDP daga gadon mulki a shekarar 2015.
Atiku wanda ya yi maganar a Yola fadar Jihar Adamawa inda ya gudanar da bikin Babbar Sallah, ya ce: “A gaskiyar magana, har yanzu ni dan Jam’iyyar APC ne; kuma da ni aka assasa ta ciki har da kamfe har aka samu nasara. Amma abin bakin ciki jim kadan da kafa gwamnati; sai aka jingine ni, babu wata dangantaka a tsakanina da gwamnatin, ba a taba tuntubata ba koda sau daya domin a ji ta bakina a kan wani abu, ni ma sai na koma gefe. Sun yi amfani da kudinmu da tasirinmu don kaiwa a inda suke, amma kusan shekara uku ga halin da muke ciki.”
Atiku ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan nasarar da ya samu a yaki da Boko Haram, sai dai har yanzu da sauran lokacin yin murna saboda gwamnatim ta gaza a fannoni da dama.
“Eh, an samu nasarori da dama amma cikakkiya ba, domin ’yan ta’addan Boko Haram suna nan suna ta’asa, suna kashe mutanenmu kuma kananan hukumomi da dama a Borno da Yobe har yanzu suna da karfi a cikinsu. Mutane ba za su iya bugun kirji su koma garuruwansu ba. Abin yana girgiza ni; ban taba tsammanin cewa Najeriya za ta dauki dogon lokaci tana yaki da Boko Haram har na shekara biyar ba. A lokacin da muka yi yakin Biyafara wanda ya fi zama mai matsala saboda yananyin Kudu, amma sojoji sun samu nasara a cikin wata 30. Amma a nan muna dogon yaki da Boko Haram, kuma babu alamun lokacin kawo karshensa,” inji Atiku.
Game da yaki da cin hanci da rashawa, tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce, an samu ’yar nasara kadan a wannan fage. “Mutane nawa ne aka kama aka hukunta aka daure? Nawa aka kwato daga barayin gwamnati? Lokacin da muka kama mulki a 1999, na tuna mun kwato tsakanin Dala biliyan 4.5 zuwa biliyan 4.7 daga wadanda suka sace su a lokacin (marigayi Sani) Abacha,” inji shi.
kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Jam’iyyar APC kan korafin Atiku bai samu nasara ba, domin Sakataren Jam’iyyar APC ta kasa, Alhaji Mala Buni bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba kuma bai amsa sakon tes da aka aike masa a shekaranjiya Laraba da daddare ba.
Mutane da dama da suke kusa da Atiku sun ce suna aiki domin ganin Atiku ya koma Jam’iyyar PDP, wadda suke ganin ita ce suke da tabbacin za ta kasance gadar da za ta kai shi ga cimma burinsa na neman zama Shugaban kasa.