2019: Yadda gwamnonin APC suka raba gari da manyan ’ya’yan jama’iyyar
A daidai lokacin da zaben badi ke dada karatowa wadansu daga cikin gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan sun raba gari da wadansu manyan ’ya’yan jam’iyyar ciki har da tsofaffin gwamnoninn jihohinsu da sanatoci da sauran jiga-jigan jam’iyyar. Takaddamar ta kaure ne a kan wadanda za su zama gwamnonin jihohi a daidai lokacin da […]

A daidai lokacin da zaben badi ke dada karatowa wadansu daga cikin gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan sun raba gari da wadansu manyan ’ya’yan jam’iyyar ciki har da tsofaffin gwamnoninn jihohinsu da sanatoci da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Takaddamar ta kaure ne a kan wadanda za su zama gwamnonin jihohi a daidai lokacin da wa’adin wadansu gwamnoni ke karewa ko gwamnonin da ba su dasawa da iyayen gidansu na siyasa ko abokan hamayyarsu a jihohin ko kuma gwamnoni masu barin gado da suke son kasancewa sanatoci.
Jihohin da lamarin ya fi muni su ne Legas da Zamfara da Nasarawa da Ogun da Sakkwato da sauransu.
Jihar da takaddamar ta fi zafi a baya-bayan nan ita ce Jihar Nasarawa inda ake samun takun-saka a tsakanin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura da tsohon Gwamnan Jihar Sanata Abdullahi Adamu, inda a shekaranjiya Laraba Gwamna Al-Makura ya ce zai kaddamar da bincike a kan gwamnatin Abdullahi Adamu bayan shekara 12 da gushewarta.
Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltar Nasarawa ta Yamma ya zargi Gwamna Al-Makura da yunkurin kawar da shi daga Majalisar Dattawa ce saboda ya ki goyon bayan yunkurin da Gwamnan ke yi na tilasta wani dan takara a Jam’iyyar APC a zaben Gwamna mai zuwa.
Sanata Adamu, ya bayyana haka ne a ranar Asabar a garin Keffi, lokacin da yake ganawa da shugabannin jam’iyyar na unguwanni da kananan hukumomin mazabarsa, inda ya ce babu wanda yake kalubalantarsa a takarar Sanata har zuwa ranar 9 ga Satumba, lokacin da Gwamna Al-Makura ya umarci Kwamishinansa na Ilimi, Tijjani Ahmed, ya sayi fom din tsayawa takarar Sanata don fafatawa da shi.
Sanata Adamu ya sha alwashin “koya wa Gwamnan darasi a fagen siyasa kan goya wa wani baya ya kalubalance shi a zaben fitar da gwani.”
“Ni Abdullahi Adamu dan A’isha, ban taba cin amanar APC ba, kuma ban taba cin amanar Al-Makura ba; duk wanda ya ci amanata zai yi nadama. A siyasar Nasarawa, musamman a mazabar sanatata, wane ne Tijjani da zai kalubalance ni? Na dauki lokaci da karfina wajen gina APC a Jihar Nasarawa, don haka ba zan bari wani ya tozarta ni a APC ba,” inji shi.
Nan take Gwamna Al-Makura ya mayar da martani kan korafin Sanata Adamu, inda ya ce, ba a sarki biyu a gari daya, tare da bayyana cewa yanzu jihar ba ta sha’awar siyasar ubangida. Ya ce, idan Sanata Adamu ya kuskura ya ce zai yi wani ganganci, to zai yi masa ritaya daga siyasa.
Gwamnan yana magana ne ta bakin Kakakinsa, Yakubu Lamai, wanda ya ce Gwamnan yana da ’yancin ya goyi bayan duk dan takarar da yake so, kuma yana girmama tsohon Gwamnan sosai, don haka lokaci ya yi da zai mutunta harkokin siyasarsa.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa a makon jiya Gwamna Al-Makura ya ziyarci Sanata Adamu a Abuja inda ya gabatar masa da Injiniya Abdullahi Sule a matsayin dan takarar da ya fi so ya gaje shi, matsayin da Sanata Adamu ya ki amincewa da shi, inda ya ce a bar dukan masu son tsayawa takara su gwada farin jininsu.
Gwamna Al-Makura yace kwamitin da zai kafa zai binciki wasu kwangiloli da ayyukan tsohuwar gwamnatin Abdullahi Adamu. Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne lokacin da yake rantsar da wadansu manyan sakatarori uku a Gidan Gwamnati da ke Lafiya, inda ya ce Jihar Nasarawa ta dukan ’ya’yanta ne don haka ba za a bar ta a hannun “masu kaka-gida wadanda in abu bai yi musu dadi ba za su iyayin komai don rusa shi.” Gwamnan ya ce shi ne jagoran Jam’iyyar APC a jihar kuma yana da ’yancin zabi, kuma duk wanda yake son ya gaje shi ya sani lokacin siyasar ubangida ta zo karshe.
Sai dai Sanata Adamu ya nuna mamaki kan yadda Gwamna Al-Makura zai tado batun bincikar gwamnatinsa bayan kusan shekara 12 da barin mulki, inda ya bayyana hakan da dabarar kawar da hankalin jama’a. “Batun shi ne shi (Al-Makura) yana kokarin ya tilasta dan takara a APC a jihar, kuma na saba masa a kai tare da ba shi shawarar da ta kamata. Sai yake ganin saba masa fito-na-fito ne da shi, shi ya sa ya tayar da kurar fada,r” inji shi.
A Jihar Zamfara kuwa wadansu ’yan bangar siyasa ce suka kai farmaki ga ayarin Gwamna Abdulaziz Yari a daidai shataletalen Lalan da ke Gusau, fadar jihar. Wannan jifa tana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun daga jijiyar wuya bayan da masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar su bakwai a Jam’iyyar APC suka gudanar da gangamin nuna rashin amincewa da yadda Gwamna Yari ya bayyana Kwamishinan Kudi na Jihar Alhaji Mukhtar Shehu Idris, a matsayin dan takarar da aka yi matsaya a kansa.
A ranar 10 ga Satumba ne Gwamna Yari ya ayyana Mukhtar Shehu Idris a matsayin dan takarar da aka yi ittifaki a kansa a taron da shugabannin kananan hukumomi da wadansu ’yan siyasa da dama suka halarta a Gusau.
Kafin wannan mataki Mataimakin Gwamnan Jihar Malam Ibrahim Wakkala da Kwamishinan Ilimi Alhaji Muttaka Rini da dan Majalisar Wakilai daga mazabar kauran Namoda da Birnin Magaji, Alhaji Aminu Sani Jaji sun nuna sha’awar tsayawa takarar. Wakkala wanda ya sayi fom dain takarar tun shekara uku da suka gabata aka rika jita-jitar shi za a bai wa kujerar kan wani shiri a tsakanin Yari da magabacinsa Sanata Yarima.
A gefe kuma ga Sanata Kabiru Marafa wanda ba sa dasawa da Gwamna Yari da shi ma ke son tsayawa takarar Gwamnan.
A Jihar Legas kuwa har yanzu tana kasa tana dabo ne ga Gwamna Akinwumi Ambode, bayan da aka yi zargin sun yi hannun riga da Uban Siyasar Jihar kuma Jagoran Jam’iyyar APC ta kasa Asiwaju Bola Tinubu.
Wakilinmu ya ce masu fashin bakin siyasa na ci gaba da yin hasashen abin da ka iya faruwa da Jam’iyyar APC a jihohin Legas da Ogun bayan da rikicin cikin- gida ya barke a tsakanin Gwamna Ambode da Cif Bola Tinubu, inda ake rade-radin Tinubu ba ya goyon bayan Gwamna Ambode don komawa Gwamna a 2019. Wannan mataki ya sanya fitowar mutum biyu masu nema su mulki jihar a karkashin Jami’iyar APC da suka hada da Babajide Sanwo-Olu wanda ake ganin yana samun goyon bayan Bola Tinubu.
Alhaji Ado Shu’aibu dansudu, daya daga cikin masu fashin baki a al’amuran siyasa, ya shaida wa Aminiya cewa rikicin Gwamnan Legas da jagoran Jam’iyyar APC abu ne da ba zai haifar wa jam’iyyar da mai ido ba, kuma wata dama ce da Jam’iyyar PDP za ta iya tsintar dame a kala, kamar yadda ya faru a lokacin rikicin cikin-gida na tsohuwar Jam’iyyar SDP a tsakanin Agbolajobi da Dapo Saromi; inda Sa Micheal Otedola ya zama Gwamnan Legas a shekarun 1990.
“A wanccan lokacin, duk da cewa Jam’iyyar SDP na da goyon bayan jama’ar Legas da fiye da kashi 80 cikin 100, rikicin cikin-gida ya sa ta rasa jihar, don haka ga dukan alamu dan takarar Jam’iyyar PDP, wato Otedola na iya tsintar dame a kala kamar yadda mahaifinsa Micheal Otedola ya tsinta,” inji dansudu.
Sai dai bayanan da sukie fitowa a baya-bayan nan sun nuna cewa akwai yiwuwar Bola Tinubu ya yafe wa Gwamna Ambode, bayan da shugabannin Jam’iyyar APC ta kasa suka matsa masa cewa ya goyi bayan Ambode. Wata majiya ta ce wani zama da Shugaba Buhari ya halarta da wadansu gwamnonin APC a wurin taron dan takarar Gwamna a zaben Jihar Osun da za a gudanar gobe ne shugabannin jam’iyyar suka roki Tinubu ya yafe wa Ambode ya sake tsayawa takara karo na biyu bayan da wadansu tsofaffin gwamnonin yankin Yarbawa suka fara yunkurin sulhunta mutanen biyu.
Tuni dai PDP ta fara shirin mika wa Ambode tikitin yi mata takara idan APC ta hana shi. A wani gangami da Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Legas Folorunso Owolabi ya jagoranta a jihar, kira ya yi ga Gwamna Ambode ya koma jam’iyyarsu, inda ya ce za su ba shi takarar Gwamnan Jihar, domin lokaci ya yi da jama’ar jihar za su dawo daga rakiyar jama’iyya mai mulki, lura da rigingimun cikin gida da suka dabaibaye ta.
“Mulkin dimokuradiyya ba mulkin mallaka ba ne da wadansu tsirari za su rika juya akalar mulkin yadda suka ga dama,” inji shi.
Kazalika a Jihar Ogun ma akwai dambarwa, inda ’ya’yan Jam’iyyarAPC suka yi zanga-zangar nuna rashin goyon bayansu ga zabin da Gwamna Ibikunle Amosun ya yi, kan wanda zai gaje shi, wanda suke gani ba sananne ba ne kuma ba gogagge ba a siyasar jihar.
Gwamnan ya bayyana dan Majalisar Wakilai daga mazabar Egbado ta Kudu da Ipokia, Mista Adekunle Akinlade a matsayin dan takarar da aka yi muwafaka a kansa daga cikin ’yan takara 10 don tsayawa wa APC takarar Gwamnan Jihar.
Idan al’amura ba su daidaita a jam’iyyar ba, masana siyasar jihar na ganin dan takarar Jam’iyyar ADC ka iya tsintar dame a kala domin al’ummar jihar sun fi saninsa da karkata gare shi, saboda ya yi takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP sau biyu, inda ya fafat da Gwamna mai barin gado. Don haka muddin Gwamnan Jihar ya tursasa dan takarar, Jam’iyyar APC za ta samu babbar matsala.
A Jihar Sakkwato ma rudani ya mamaye Jam’iyyar APC kan tsayar da dan takarar Gwamna, lamarin da ya sa magoya bayan jam’yyar suka rabe biyu tare da zargin juna.
kungiyoyin matasan APC suna dora laifi a kan jagoran jam’iyyar a jihar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da shugabanta Alhaji Isa Sadik Achida suna zarginsu da yunkurin dora dan takarar da suke ganin ba za a iya samun nasara a zaben Gwamna na badi ba.
Sun yi zargin cewa Sanata Wamakko yana son tsayar da Mataimakin Gwamna Alhaji Ahmad Aliyu maimakon tsohon Kwamishinan kananan Hukumomi Alhaji Faruk Malami Yabo.
Rudanin ya samu ne bayan da Malam Bashir Gidan Kanawa wani makusancin Sanata Wamakko ya sanar a shafinsa na Facebook cewa an yi matsaya cewa Mataimakin Gwamna Ahmad Aliyu ne APC za tsayar takarar Gwamna, lamarin da ya sa magoya bayan jam’iyyar suka yi masa ca tare da nuna rashin goyon bayansu ga zabin.
A Jihar Yobe kuwa masu neman tsayawa takarar Gwamna a APC su uku ne suka sa kafa suka shure ayyana Sakataren Jam’iyyar APC ta kasa Alhaji Mai Mala Buni a matsayin dan takarar Gwamna, inda suka ce Gwamna Ibrahim Gaidam shi kadai ya yi gaban kansa. Wannan takaddama ta jawo siyasar jihar ta yi zafi, musamman a tsakanin Gwamna Gaidam da uban siyasar jihar Sanata Bukar Abba Ibrahim, wanda Gwamnan ke neman kujerarsa. Sai dai bayanan da suke fitowa a baya-bayan nan sun nuna cewa an samu maslaha a tsakanin Sanata Bukar Abba da Gwamna Gaidam, idan kuma maslahar ta kasa tabbata, Jam’iyyar PDP da ta dauki shekara da shekaru tana adawa a jihar tana iya yi wa APC shigar sauri ta amshe kujerar a karon farko.
Akwai dai masu son tsayawa takarar Gwamna da suka hada da Alhaji Sidi Yakubu Karasuwa da Alhaji Aji Kolomi da Alhaji Ibrahim Bomoi.
A Jihar Imo ma APC ta dade tana fama da takaddama kan wanda zai tsaya mata dan takara bayan da Gwamna Rochas Okorocha ya bayyana Shugaban Ma’aikatansa kuma surukinsa, Uche Nwosu da wanda zai gaje shi. Sai dai Mataimakin Gwamnan, Eze Madumere ma ya ce zai tsaya takarar a Jam’iyyar APC. Sannan ga Injiniya Chuks Ololo da ke auren kanwar Gwamnan mai suna Ogechi ma ya ce shi ma yana so, kafin Sakataren Gwamnatin Jihar Mista George Eche, ya biyo baya.