2023: A ba Osinbajo dama ya dora daga inda Buhari ya tsaya – Matasan Arewa

Matasan sun ce Osinbajo ya fi kowane dan takara nagartar zaman Shugaban Kasa

2023: A ba Osinbajo dama ya dora daga inda Buhari ya tsaya – Matasan Arewa

Mataimaki Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

A yayin da babban zaben 2023 ke ci gaba da karatowa, Gamayyar Kungiyar Jakadun Arewa maso Yamma (NAFO), ta yi gangamin goyon bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, don zama sabon angon Najeriya.

NAFO ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a ranar Asabar, ta hannun Shugabanta, Barista Halimatu Sadiya Muhammad.

Sanarwar ta ce, “Mu, Jakadun Arewa maso Yamma (NAFO), mun hade kanmu tare sa zabar Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai ci gaba da jan ragamar Shugabancin Najeriya.

“Muna bukatar mutumin da zai samar da hadin kai a tsakanin ’yan kasa tare da kore rarrabuwar kai da kabilanci a 2023.

“Kazalika yana da kyau a ce mulki ya koma Kudanci a 2023 don tabbatar da daidaito da adalci ga kowane yanki na kasar nan,” inji ta.

Har wa yau, ta kara da cewar akwai bukatar bai wa Osinbajo dama don ci gaba da ayyukan da shugaba Buhari ya faro.

“NAFO na son a bai wa Osinbajo dama don dorawa da ayyukan alheri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa wannan kasa tamu da kuma jam’iyyarmu ta APC.

“Alamu sun nuna yadda mai girma Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya zama zakaran gwajin-dafi kan yadda ya ja ragamar kasar nan a duk lokacin da Shugaba Buhari ya yi tafiya.

“Wannan ya nuna irin nagarta da kwazo da gogewa da ya ke da shi a fagen siyasa.”

Kazalika, shugabar ta ce akwai bukatar kau da banbanci don zabar wanda ya cancanci zama gwarzon Najeriya a 2023.

“Babu shakka muna bukatar samun wanda zai kawo karshen tashin hankulan da ke faruwa, rikicin kabilanci da na addini da muke fama da su a kasar nan.

“Mataimakin shugaban kasa mutum ne mai son arewa kuma muna ganin zai iya mulkar kasar nan ba tare da nuna wariya ga kowace shiyya ba,” kamar yadda ta bayyana.

A makon da ya gabata ne mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar Shugaban Kasa a APC a zaben 2023.