2023: Ahmed Lawan zai bi sahun masu zawarcin kujerar Shugaban Kasa a APC
Ana sa ran Ahmed Lawan zai sayi fim din takarar ranar Laraba
An samu baraka tsakanin Sanatoci kan kiran da ake musu su goyi bayan Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan, a matsayin dan takarar maslaha na Shugaban Kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
Ahmed Lawan dai wanda tun shekarar 1999 yake a Majalisar Dokoki ta Kasa ya shirya tsaf domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a hukumance a cikin makon nan, kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar wa Aminiya.
Sai dai Shugaban Majalisar ta Dattawa ya shaida wa ’yan jarida ranar Litinin cewa Allah ne kadai zai iya sanin makomar shi a siyasance.
Ana dai tunanin wasu jiga-jigan ’yan siyasar Arewa ne ke kokarin cicciba manufofin takarar tashi.
An dai fara zaben shi ne a matsayin mamba a Majalisar Wakilai a shekarar 1999, kafin daga bisani ya koma Majalisar Dattijai a 2007, kuma tun lokacin ake damawa da shi a cikinta.
Aminiya ta gano cewa gabanin ayyana takarar tasa, akwai kokarin da ake na amincewa da dan siyasar dan asalin Jihar Yobe a matsayin dan takarar maslaha na Majalisar.
Daga cikin masu kokarin ganin Ahmed Lawan din ya kai ga gaci sun hada da Sanata Yusuf Yusuf (APC, Taraba) da Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (APC, Neja) da kuma tsohon Sanata Abdullahi Gumel.
Sai dai da alama yunkurin ya raba kan majalisar mai mambobi 71 daga APC mai mulki, 37 daga PDP da kuma daya daga YPP.
Idan ya ayyana tsayawa takarar, zai bi sahun ’yan takara irin su Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da na Kwadago, Chris Ngige da Gwamnonin Jihohin Kogi da Ekiti da Kuros Riba Ebonyi da dai sauransu.
Jam’iyyar APC dai ta tsayar da 30 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar gudanar da zaben fid-da gwaninta na takarar Shugaban Kasa a zaben mai zuwa.