2023: Akan da Akpabio za su daukaka kara kan hana su takara

’Yan takarar na Jam’iyyar APC sun kudiri niyyar daukaka kara kan hukuncin kotun da ta soke takararsu

2023: Akan da Akpabio za su daukaka kara kan hana su takara

’Yan takarar Jam’iyyar APC, Sanata Akan Udofia da Sanata Godswill Akpabio, za su daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke na hana su shiga zaben 2023.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Uyo ta soke zaben fid-da-gwanin APC tare da bayyana cewa, Akanimo Udofia bai cancanci tsayawa takarar Gwamnan Jihar Akwai Ibom a jam’iyyar ba.

A gefe guda kuma, Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta umarci hukumar zabe ta soke takarar Sanata Akpabio a zaben 2023, inda ta ce kotun farko ta yi kuskuren ayyana shi a matsayin dan takarar APC.

Sai dai ’yan takarar biyu sun yi fatali da hukuncin da kotun ta yanke na hana su shiga zaben 2023.

“Obong Akanimo Udofia na kara mamaki, kuma yana da kwarin gwiwar cewa tabbas da shi za a yi zabe a matsayin dan takarar gwamna a Jam’iyyar APCna 2023 kuma zai lashe tare da goyon bayan al’ummarmu.

“Babu wani shakku game da takararsa, muna da kwarin gwiwa sosai a bangaren shari’armu, kuma za mu daukaka kara a kan hukuncin wannan kotu.

“Muna kira ga al’ummar Jihar Akwa Ibom da magoya bayanmu da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum,” in ji shi.

Da yake magana ta wata sanarwar, Akpabio, ya yi mamakin dalilin kotun na soke takararsa.

“Hankalina ya karkata ga hukuncin da kotun daukaka kara a Abuja ta yanke, ta umarci INEC ta cire sunana daga jerin ’yan takarar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a Jam’iyyar APC a zaben 2023.

“A yayin da ake jiran hukuncin kotun, ya kamata a ce ni lauya ne ta hanyar horarwa kuma mai bin doka da oda a kasar nan kuma ina bin dokokinmu da hukunce-hukuncenmu don daukar matakin da ya dace.

“Ina sane da cewa Kotun Kolin Najeriya ce ta yanke hukunci a kan wasu hujojji, don haka ina kira da babbar murya ga magoya bayana da ’ya’yan Jam’iyyar APC da daukacin al’ummar mazabata da su kwantar da hankalinsu, su bi doka da oda, yayin da suke ci gaba da yakin neman zaben APC a Akwa Ibom ta Yamma da kuma Najeriya baki daya,” in ji shi.