2023: Al-Mustapha: Na hannun daman Abacha da ke son haye kujerar Buhari
Ko wacce irin dama yake da ita ta lashe zaben?
Ana yi wa Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar Action Alliance (AA) kirari da dashi mai dogon rai.
Wannan na da alaka da rawar da ya taka a matsayinsa na babban jami’in soja da yadda ya samu nasara a fafatawar da ta shafi shari’a da siyasa da tsaro.
- Mali ta yi wa sojojin Cote d’ivoire 49 afuwa
- ’Yan bindiga sun sace gomman fasinjojin jirgin kasa a Edo
Al-Mustapha wanda tsohon Manjon soji ne kuma kwararren jami’in leken asiri ya yi aiki a matsayin Babban Jami’in Tsaro na marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha wanda ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa 1998.
Na hannun daman Abachan, an haifi Al-Mustapha ne a watan Yulin 1960 kuma ya yi fice wajen tsayuwar daka da kwazo da sadaukarwa. Ya samu horon soja ne a bangaren leken asiri.
Ya rike mukamai masu muhimmanci a bangaren tsaro na Hukumar Leken Asiri ta Sojin Najeriya (DMI) da Runduna ta 82 da Hedikwatar Soji da Ma’aikatar Tsaro da sauransu.
Ya fara neman ilimi a garin Nguru da ke Jihar Yobe, inda daga nan ya shiga Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin Soja (NDA) ya zama sojan Najeriya a 1983.
Sakamakon rasuwar Abacha a 1988, Al-Mustapha ya taro manyan sojoji don kauce wa rikicin magaji.
Janar Abdulsalami Abubakar ya zama Shugaban kasa ranar 9 ga Yunin 1998, kuma aka cire Al-Mustapha sannan aka tsare shi.
A daya daga cikin tattaunawa da shi da wakilinmu ya karanta, Al-Mustapha ya ce, “An kama ni a ranar 21 ga Oktoban 1998, saboda wani bidiyo amma ba saboda marigayiya Kudirat Abiola ba. A lokacin iyalan Abiola suna da matukar kusanci gare ni.
“Amma sai wani abu ya faru, wanda kyamara ta dauka a fadar Shugaban kasa. Sai suka so sa dauke bidiyon su kona shi ta yadda ’yan Najeriya ba za su san abin da ya faru ba.
Wannan shi ne tushen shiga ta matsala. Mutane da dama musamman lauyoyi sun karbi kudi daga wadanda suke neman kaset din wadanda suka mulki Najeriya.
“Sun je rediyo da talabijin sun yi ta zagina, maimakon su je kotu, saboda an biya su ne su yi haka. Amma ba su san abin abin da yake faruwa a kotu ba.
“An gurfanar da ni a gaban alkalai 14 a Legas. Da zarar an yi kusan yanke hukunci, sai su dakatar su canja kotu. Na shafe shekara 15 a cikin wannan hali. Daga cikin wadannan shekaru 15, shekara biyar da wata biyu ina tsare ne a hannun hukumomin tsaro ana gallaza min. Sauran na yi su ne a tsakanin kurkukun Ikoyi da Kirikiri da na Jos,” in ji shi.
Rawar da ya taka a zamanin Abacha
Janar Sani Abacha ya karbi mulki ne a 1993, kuma ya nada Al-Mustapha a matsayin shugaban tsaronsa daga ranar 17 ga Nuwamban 1993 zuwa 8 ga Yunin, 1998.
A karkashin wannan matsayi shi ke kula da tsaron gwamnatin kuma ya kakkafa hukumomin tsaro da dama.
Akwai bayanan da suke cewa shi ne yake juya dukkan rundunonin tsaron Abacha ciki har da dogaransa da wata bataliya ta musamman da ake kira “Strike Force” da aka tura Libiya da Koriya ta Arewa don samun horo.
Sauran hukumomin tsaro a lokacin sun hada da Ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro (NSA) a karkashin Sama’ila Gwarzo da Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA) da Hukumar Leken Asiri ta Soji (DMI) da Hukumar Tsaro ta kasa (SSS).
Hatta manyansa a soji suna girmama shi saboda sanin kusanci da alakarsa da Abacha a lokacin mulkin da kuma yadda yake iya sauya al’amura zuwa wata fuskar.
Siyasa da mulki
Yana da muhimmanci a bayyana cewa Al-Mustapha ne ya kula da sake fasalin Najeriya zuwa shiyyoyin siyasa shida.
A karkashin haka ya samu dimbin masu leken asiri da masu bayar da bayanai a sassan kasar nan. Shiyyoyin siyasar shida su ne, Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Arewa ta Tsakiya ta kunshi jihohin Benuwai da Neja da Kwara da Kogi da Filato da Nasarawa. Sai Arewa maso Gabas mai jihohin Adamawa da Borno da Bauchi da Yobe da Taraba da Gombe.
Arewa maso Yamma na da jihohin Jigawa da Kebbi da Katsina da Sakkwato da Kaduna da Kano da Zamfara. Sai Kudu maso Gabas mai jihohin Abiya da Imo da Enugu da Anambra da Ebonyi. Kudu maso Kudu na da jihohin Akwa Ibom da Edo da Ribas da Kuros Riba da Bayelsa da Delta, yayin da Kudu maso Yamma ke da jihohin Legas da Oyo da Osun da Ekiti da Ondo da kuma Ogun.
Sojan leken asiri
Al-Mustapha ya samu horo ne a matsayin sojan leken asiri.
Ya rike mukaman shugabanci da dama a Ma’aikatar Harkokin Waje da rukunonin tsaro na Hukumar Leken Asiri ta Soji (DMI) da Runduna ta 82 da Hedikwatar Soji da Ma’aikatar Tsaro da kuma Fadar Shugaban kasa.
Kuma ya yi aikin bibiyar harkokin leken asiri kuma bincike a kan yunkurin juyin mulki akalla sau biyu ya sa hankalin Janar Abacha ya koma kansa.
Ya gudanar da ayyuka a Chadi da Laberiya da Bakassi da Gambiya da Saliyo. Manjo Al-Mustapha ya sha nanata cewa yana tsaye kan rantsuwar kare Shugaban kasa da iyalansa da kuma mazaunin gwamnati.
Hukuncin kisa
A ranar 3o ga Janairun 2012 ne aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya shi da Lateef Sofolahan wani jami’in karbar baki na kwamitin yaki zaben Moshood Abiola.
Su biyun an yanke musu hukunci ne kan kisan Kudiratu Abiola, matar Moshood Abiola wanda ake ganin shi ne ya lashe zaben Shugaban kasa na 1993.
An yanke wa Al-Mustapha hukunci ne bisa zargin ya ba wani jami’in tsaro umarnin ya kashe Kudirat, amma ya musanta hannunsa a kisan nata da ya auku a 1996, inda ya ce an tilasta shi ne ya yi bayani na farko.
A wata tattaunawa Al-Mustapha ya ce, “Saboda wahalar da aka ba ni ne na yi furucin. Idan wanda ake tuhuma ya hadu da cin zarafi, kuma halin da aka sa mutum a ciki ya yi muni, ba za a yi amfani da abin da ya fada a wannan shari’a ba.
“An rika yi min shifta ne. Kuma na amince in yi haka ne don a kai ni kotu ko kurkuku in samu ganin lauyoyina. An shafe shekara guda ban ga lauyoyina ko iyalaina ba,” in ji shi.
Sai dai alkalin kotun, Mai shari’a Mojisola Dada, ba ta gamsu da hujjarsa ba, inda ta yanke hukuncin cewa su biyun ne suka kashe Kudirat a 1996 da bindiga mai sarrafa kanta don haka za a kashe su ta hanyar rataya.
Sako Al-Mustapha
A ranar 12 ga Yulin 2013, aka sako Al-Mustapha daga kurkukun kirikiri da ke Legas, sakamakon wanke shi da sallamarsa da Kotun daukaka kara ta yi.
Kotun daukaka karar da ke Legas ta soke hukuncin kisan da aka yanke wa Al-Mustapha da Sofolahan.
Al-Mustapha ya rika daga hannu ga masoya da suka hallara a bakin kurkukun yana cewa: “Na gode Allah, na gode Allah,” lokacin da ake shirin sa shi a wata mota kirar Jeep da ta tafi da shi.
Yadda ya zama dan takarar Jam’iyyar AA
A watan Yunin 2022 ne Al-Mustapha ya zama dan takarar Jam’iyyar AA a wajen zaben fid-dagwanin da ta gudanar.
Ya kayar da abokin takararsa Samson Odupitan bayan da wasu ’yan takara biyu, Feild Osakwe da Tunde Kelani suka janye daga tarkarar tare da nuna goyon bayansu gare shi.
Ya samu kuri’a 506 ya kada Odupitan wanda ya samu kuri’a 215. Shugaban Jam’iyyar AA, Mista Kenneth Udeza ya ce dalaget 842 aka tantance don zabar dan takarar inda aka yi zaben kato bayan kato.
A shekarar 2019, Al-Mustapha ya tsaya takarar Shugaban kasa ne a karkashein Jam’iyyar PPN, amma ya sha kaye a hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Magance rashin tsaro
Al-Mustapha ya shaida wa dalaget cewa gogewarsa a aikin soja wanda ya shafe shekara 35 da kuma aikinsa tare da Abacha za su ba shi dama ya magance matsalar tsaro in aka zabe shi a zaben bana.
“Ni mutum ne mai saukin kai, kuma ina da kwarewar da zan iya magance matsalar tsaro da take addabar kasar nan,” in ji shi.
A wata tattaunawa da Sashin Hausa na BBC a kwanan nan, ya ce, zai sake fasalin yadda sojoji suke aiki da yadda ake tunkarar barazanar tsaro, inda ya ce, za a samu sabon kwazo da sadaukarwa a tsakanin sojojin a karkashin mulkinsa.
Ya ce, “Idan na zama Shugaban kasa, zan zauna a Sambisa; zan rika zama a can a karshen mako da lokacin hutu in ga ko wani zai iya taba ni. Zan magance matsalar rashin tsaro ko da wa ke da hannu a ciki.
“Dubi ayyukan ta’asa na Boko Haram, na rantse idan aka gaza magance ta a cikin wata shida zan rage mukaman dukkan manyan hafsoshin soja in kora su gida. Za a hukunta su kuma tilas su dawo da kudin da aka ba su. Kuma zan bincike su.
“Sojojin Najeriya yanzu sun zama ’yan sanda, ka san yadda ’yan sandanmu suka lalace wajen cin hanci. Don haka cikin wata shida zan kawo gyara kan yadda sojojin Najeriya suke aiki ta yadda za su tunkari barazanar tsaro da ka iya tasowa cike da kwazo da sadaukarwa.”
Dama
Masu sharhi sun ce Al-Mustapha dan takarar Shugaban kasa ne mai kyau, amma motar da ya hau yake takarar ce ba a san da ita ba.
Wasu sun ce zai ci gaba da zama wanda ake damawa da shi a harkokin kasar nan koda bai lashe zaben bana ba.
Wani mai nazarin siyasa Cif Jackson Lekan Ojo ya shaida wa Aminiya ta tarho cewa, “Al-Mustapha yana da matukar kwarewa da ilimi da kwazo da tsari, kuma yana da masaniya kan batutuwan da suka shafi bunkasa da ci-gaban kasa. Yana da abubuwan da ake nema daga Shugaban kasa.
“Ya san abubuwa da dama a kan Najeriya – tattalin arziki da tsaro da hadin kan kasa. Sai dai abin da kawai zai kawo masa cikas, shi ne ya shiga jam’iyyar da ba a san ta sosai a Najeriya ba, ba ma kula da daidaiku, mun fi kula da jam’iyyun siyasa.
“Da a ce muna kasar da take girmama direba ne, Al-Mustapha yana iya kasancewa daya daga cikin na gaba a ’yan takarar Shugaban kasa. Don haka in wani ya ce, ya dace da zama Ministan Tsaro ko Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro, suna fadin haka ne saboda jam’iyyarsa ba sananniya ba ce, zai yi wuya ya lashe zaben,” in ji shi.
Sai dai a yayin da zaben Shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu ke karatowa kuma kurar siyasa take dada kadawa, abin da ya rage shi ne a zuba ido a ga yadda Manjon mai ritaya zai sakalo ta da ’yan takarar sauran jam’iyyun.