2023: APC ta tsawaita lokacin sayar da fom din takara
Yanzu ranar 12 zuwa 14 ga watan Mayu za a gudanar da taron zaben daliget
Jam’iyyar APC mai mulki ta tsawaita lokacin da ta sanya na sayar da fom din neman takararta a zaben 2023 da kwana hudu.
Karin wa’adin ya zo ne kimanin awa 48 kafin cikar wa’adin da ta sanya da farko na kammala sayar da fom din a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayun da muke ciki, gabanin zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyar.
- Shugabannin PDP sun ba wa hamata iska a Kano
- Sojoji sun yi raga-raga da sansanonin Boko Haram 24 a Borno
Sanarwar da Sakataren Yada Labararn jam’iyyar, Barist Felix Morka, ya fitar a ranar Laraba ta ce an tsawaita lokacin sayar da fom din da kwana hudu, zuwa ranar Talata 10 ga watan Mayun da muke ciki.
Kazalika sabon jadawalin tsarin sayar da fom din da Sakataren Tsare-tsaren jam’iyyar, Sulaiman Muhammad Argungu, ya fitar ya nuna ranar Laraba 11 ga watan Mayu za a rufe karbar fom din neman tsayawa takara da aka cike.
A sakakamon haka, yanzu ranar 12 zuwa 14 ga watan Mayu za a gudanar da taron zaben daliget a dukkan matakai — kananan hukumomi, jiha da kuma tarayya.