2023: Dalilina na janyewa daga takarar dan majalisa — Alan Waka

Ya ce har yanzu babu wata cikakkiyar shaidar takara daga jam’iyyar tasa

2023: Dalilina na janyewa daga takarar dan majalisa — Alan Waka

Fitaccen mawaki a Masana’antar Kannywood, Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da ALA ya ce ya janye daga takarar kujerar Majalisar Wakilai domin wakiltar karamar Hukumar Nassarawa dag a Jihar Kano.

A cewarsa, “Na sha bayyana wa mutane cewa ni dan takara ne. Amma fa kamar yadda yake fada, ni ma haka ji kawai nake yi domin ba ni da wata takarda da nake nuna cewa ni dan takara ne.

A yau da nake magana zabe ya rage saura kwana 55 ko 56, amma ba ni da kakkarfar shaida cewa ni dan takara ne a jam’iyyar da nake takara. Jama’a Najeriya akwai doka.

A daidai wannan kafa, duba da alkawarin da muka yi da Jam’iyyar ADP cewa in muka shiga jam’iyyar za a ba mu takara a karkashin kungiyar 13d13.

Amma tun daga lokacin da aka yi wannan magana, ita kanta kungiyar ban ga wani motsi da ta yi ba na ’ya’yanta na takara.

Magana kawai muke daga wadanda ba su da hurumi. Abin da nake nufi shi ne jam’iyya ce kadai ke da hurumin mika dan takararta ga INEC.

Har yanzu ba mu samu wannan alama ko daya ba. Kuma alamomi suna cewa lokaci ya wuce.

Wannan ya sa domin kada mutum ya taka dokar kasa da INEC da ta jam’iyya ne ya sa na rubuta takardar ficewa daga jam’iyyar, kuma ba na cikin ’yan takarar na karamar Hukumar Nasarawa.”

ALA ya kara da cewa alkawarin da aka musu bai cika ba, amma shi ba ya rigima da kowa, inda ya ce dama saboda alkawarin ne ya shiga jam’iyyar, kuma ba a cika ba.