2023: Dungun da Buhari ya yi ya jefa Osinbajo da Tinubu da sauransu a duhu

Akwai sarkakiya a lamarin domin duk masu neman takara suna ganin suna da goyon bayan Shugaba Buhari.

2023: Dungun da Buhari ya yi ya jefa Osinbajo da Tinubu da sauransu a duhu

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari

Rashin cewa uffan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi a kan wanda yake so a tsakanin masu neman takarar shugabancin kasar nan a Jam’iyyar APC a zaben badi bai yi wa ’yan takarar dadi ba.

Masu ruwa da tsaki sun ce hakan na iya kawo cikas ga ’yan takarar da suka hada da Mataimakinsa Yemi Osinbajo da jagoran Jam’iyyar na Kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da sauransu.

Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa wadansu masu son yin takarar sun ki bayyana niyyarsu ce, don ganin watakila Shugaban Kasar kan iya karkata ga wani dan takarar da yake so, hakan ta sa ko Mataimakinsa Osinbajo bai bayyana niyyarsa ba, sai a ranar Litinin din makon jiya, haka Amaechi ya yi a karshen makon jiya.

Fara daga kan Tinubu, masu son tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar sai da suka sanar da kuma neman alfarmar Shugaban kafin su bayyana niyyarsu ta tsayawa.

Rashin bayyana alkiblar Shugaban Kasa, kamar yadda Aminiya ta gano, ya kara tada kura a tsakanin ’yan takarar da magoya bayansu yayin da lokacin gudanar da zaben fid-da-gwanin jam’iyyun siyasa ke karatowa.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayar da wa’adin ranar 3 ga watan Yuni, ga jam’iyyun siyasa su gudanar da zaben fitar da ’yan takara.

Zuwa yanzu, masu neman tsayawa takara tara ne a jam’iyya mai mulki da suka nuna sha’awarsu.

Wadanda suka hada da; Tinubu da Osinbajo da Amaechi da Gwamna Dabid Umahi na Jihar Ebonyi da Yahaya Bello na Jihar Kogi da hamshakin dan kasuwa Gbenga Olawepo Hashim da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da Ihechukwu Dallas Chima (IDC), yayin da Ministan Kwadago Dokta Chris Ngige ya shigo daga baya.

Wata majiya mai tushe a fadar Shugaban Kasa ta shaida wa Aminiya cewa Shugaba Buhari yana sane da masu son tsayawa takarar, kuma yana kokarin ganin bai yi gaban kansa ba, amma dai ya boye wanda yake so a zuciyarsa.

Shugaban Kasar a ranar 5 ga Janairun bana a wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, ya ce bai damu da wanda zai gaje shi ba.

A cewarsa: “Shekarar 2023 ba matsalata ba ce, ban damu da wanda zai gaje ni ba, kowa ke so ya nema, ko wane ne.”

Ya kuma kibayyana wanda ya fi so ya gaje shi, yana mai cewa idan ya bayyana ana iya cutar da shi.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce matakin da Shugaban Kasar ya dauka ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu son tsayawa takara da magoya bayansu da kuma masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyar.

Majiyar ta ce a tsarin Jam’iyyar APC, sabanin sauran mukamai, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ba wai Shugaban Kasa kadai ne zai iya zabarsa ba.

“Abin da zan iya gaya muku shi ne, yanayin da aka kawo Abdullahi Adamu, inda Shugaban Kasa ya zabe shi da kansa, wannan ba zai maimaitu ba a yanzu.

Dole ne a gudanar da zaben fid-da-gwani domin jam’iyyar ta samu nasara a 2023.

“Shugaban Kasa yana lura da wannan, don haka yake takatsantsan a kai.

Ko a yayin da ake tunkarar zabbubukan 2015, duk da masu ruwa-da-tsaki sun san cewa tikitin jam’iyyar na Buhari ne, amma sai da aka gudanar da zaben fid-da-gwani a Legas, inda ya doke Atiku da Kwankwaso da Bukola (Saraki) da Okorocha da sauransu,” inji majiyar.

Sai dai wata majiya ta ce “Da alama Shugaban Kasar bai gamsu da yin takara a tsakanin Osinbajo da Tinubu ba, amma dai karshe Tinubu ne zai samu tikitin takarar.’’

Shugaban Kasa na cikin matsi

Majiyoyi sun ce duk da cewa ya bayyana bai damu da wanda zai gaje shi ba, akwai alamun da suke nuna cewa Shugaban yana cikin tsaka-mai-wuya.

Daya daga cikinsu ta ce wadanda suka mara masa baya a lokacin da ya fi bukata da su da magoya bayansu suna ganin wannan ne lokacin da za a biya su.

Yayin da wadanda suke tare da Tinubu suke cewa suna bin Shugaban Kasar bashi, idan aka yi la’akari da irin rawar da tsohon Gwamnan Jihar Legas ya taka wajen samun nasarar Buhari a zaben 2015 da 2019.

Sai dai wadanda suke tsagin Mataimakin Shugaban Kasa suna cewa fitowarsa a matsayin Mataimaki ya kasance tamkar wata mu’ujiza ce da ta ba su damar lashe zaben 2015.

Kuma kafin zaben 2015 sau uku Shugaba Buhari yana yin, takara bai samu nasara ba. Magoya bayan Mataimakin Shugaban Kasar suna kuma cewa a matsayinsa na mutum na biyu a kasar nan, ya kamata a ba shi dama ya ci gaba da samun nasarar gwamnatin APC.

A nasu bangaren, wadanda suke bangaren tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, suna cewa ya kamata a duba dan takararsu lura da irin rawar da ya taka a matsayinsa na Babban Daraktan Kwamitin Yakin Zaben Buhari.

Yadda Obasanjo ya zabi magajinsa

Aminiya ta ruwaito cewa, a zaben 2007, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bai wa dukkan masu neman tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar PDP a wancan lokaci damar tsayawa takara.

Manyan ’yan takarar a wancan lokaci sun hada da Gwamna Jihar Ribas Mista, Peter Odili da Ahmed Mohammed Makarfi na Jihar Kaduna da Abdullahi Adamu, Nasarawa da Donald Duke, Kuros Riba da sauransu don tallata takararsu.

Amma kafin zaben fid-da gwani na Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, sai Obasanjo ya fitar da marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa wanda ke zangon mulkinsa na karshe a Gwamnan Jihar Katsina a matsayin dan takarar Shugaban Kasa duk da cewa Umarun bai nuna sha’awar tsayawa takarar ba.

Sai Obasanjo ya tattara jigajigan ’yan siyasar kasar nan don tabbatar da cewa ’Yar’aduwa ya karbi tikitin takarar jam’iyyar kuma ya ci zabe.

Marigayi ’Yar’aduwa a lokacin rantsar da shi ya amince da cewa zaben da ya kai shi ga karagar mulki na cike da kura-kurai.

Manazarta na auna take-taken Buhari

Wani masani a kan harkokin siyasa a Jami’ar Ilorin, Dokta Isiak Atanda Abdulwaheed, ya ce halin da Shugaba Buhari ya shiga wani matsayi ne mai matsi a siyasance kuma zai iya haifar wa jam’iyyar matsala.

A cewarsa, “Abin da ya kamata kowa ya sani a yanzu shi ne yadda Shugaba Buhari ya ki fitowa ya nuna cewa ga wanda yake mara wa baya.

Kuma hakan siyasa ce, hakan na nuni da cewa yana da sha’awar son wanda zai gaje shi.

Wanda, idan ba a kula ba, zai haifar da nakasu ga jam’iyyar, kuma zai iya sa wadansu daga cikin jiga-jiganta su balle daga jam’iyya mai mulki.

“Dalili kuwa shi ne, yadda al’amura suke tafiya, idan har Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya samu tikitin APC ba Tinubu ba, wanda alama a yanzu na nuna hakan na iya faruwa al’amura na iya canjawa.

“Kuma, idan har Jam’iyyar PDP ta fitar da dan takara mai karfi mai farin jini da karbuwa ga jama’a, wannan kan iya ba ta damar cin bagas a ranar zabe, ta hanyar samar da Shugaban Kasaba tare da wahala ba,” inji shi.

Wani mai sharhi a kan al’amuran jama’a, Kwamared Achike Chude, gargadi ya yi cewa akwai yiwuwar darewar Jam’iyyar APC ganin yawan masu neman shugabancin kasar zuwa yanzu.

Chude, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Joint Action Front, ya ce matakin da Shugaban Kasa ya dauka na kin amincewa da kowane dan takara na iya zama mai illa.

A cewarsa, har yanzu lamarin na da sarkakiya domin duk masu son tsayawa takara har zuwa yanzu sun ganin suna da goyon bayan Shugaban Kasar.

Ya ce, “Abin da muka lura a harkokin siyasa a Najeriya shi ne, yadda ’yan takarar da ke neman mukaman siyasa suke zuwa wajen sarakunan gargajiya don su sa masu albarka, ko su yi musu fatar alheri.

Amma a mafi yawan lokuta sarakunan ba sa ce masu, ‘Ina goyon bayanku.’ Wannan shi ne abin da muke hasashe daga Shugaban Kasa.

Idan Shugaban Kasa yana da dan takara, kuma ya bayyana shi. Idan za a iya tunawa a yayin tattaunawa da manema labarai ya ce, ‘Yana da wanda ya fi so amma ba zai fade shi ba saboda gudun kada a kau da shi.

“Abin takaddama a kan wannan Magana tasa ita ce shin kautarwar ta siyasa ce, ko ta zahiri. Akalla, dai ya bayyana cewa yana da wanda ya fi so. Yanzu wanda aka fi so din ko shi ne Tinubu?

“Ko zai iya zama Mataimakin Shugaban Kasa, kai ko zai iya zama Fasto Tunde Bakare wanda ya bayyana karara cewa shi ne zai kasance Shugaban Kasa na 16, bayan Buhari wanda shi ne na 15. Ba mu na san ko wane ne a cikinsu ba, ko kuma wani mutum ne daban a APC,” inji shi.

APC ta fitar da jadawalin zaben fid-da-gwani

A wani labarin, Jam’iyyar APC ta Kasa, ta fitar da jadawalin zaben fid-da-gwani na’yan takararata.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Sakatern TsareTsare na Jam’iyyar ta Kasa, Alhaji Sulaiman Muhammad Arugungu ta ce daga yau Juma’a za a fara sanar da jihohi game da zaben sannan a fara sayar da fom a gobe Asabar.

Za a zabi wakilan jam’iyya na kasa a ranar 9 ga Mayu mai zuwa inda za a kammala abubuwan da za su biyo baya har zuwa tantance korafi daga 12 zuwa 23 ga Mayu.

Sai kuma zaben fitar da ’yan takarar Gwamna ranar ga 18 ga Mayu na majalisun jihohi 20 ga Mayu na sanatoci 24 ga Mayu, yayin da za a yi Babban Taron Jam’iyya na Musamman da fitar da dan takarar Shugaban Kasa a ranakun 30 ga Mayu zuwa 1 ga Yunin bana.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50