2023: ‘Harin’ da aka kai wa ayarin Atiku a Borno ya yamutsa hazo
Atiku da PDP sun hakikance cewa ’yan dabar Jam’iyyar APC sun kai musu hari, a yayin da ’yan sanda ke cewa taron jam’iyyar ya gudana cikin lumana da cikakken tsaro
Zargin an kai hari ga ayarin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a ziyarar da ya kai Jihar Borno ya jawo ce-ce-ku-ce.
Atiku da PDP sun hakikance cewa ’yan dabar Jam’iyyar APC sun kai musu hari, a yayin da ’yan sanda ke cewa taron jam’iyyar ya gudana cikin lumana da cikakken tsaro.
- NAJERIYA A YAU: Me Ke Sa Tinubu Baya-baya Da Shiga Jama’a?
- Motar yashi ta muttsuke mutum 6 a Adamawa
Duk da haka ’yan sanda sun ce sun kama wani dan daba dauke dutse, a yayin da gwamnatin APC mai mulkin Jihar Borno ke zargin PDP da kirkirar karya domin neman biyan bukatun siyasa.
A ranar Laraba ce Atiku ya sake zuwa yakin neman zabe a Jihar Borno, mahaifar abokin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima.
An kai wa ’yan PDP hari —Mutanen gari
Wani mazaunin garin Maiduguri ya shaida mana a ranar cewa ’yan daba sun far wa ayarin motocin ’yan PDP a unguwar Dalori da ke kan Titin Airport a garin.
Ya ce, “A kan titin Airport Road wasu ’yan daba suka rika jifar motocin PDP, amma jami’an tsaron da ke cikin ayarin suka yi harbi a iska suka watsa su.
“Ina ganin shi ne abin da Sanata Dino Melaye ya sanya a shafinsa wai ’yan bindiga sun kai wa ayarinsu hari.”
Shi ma wani mazaunin garin da ke tabbatar da harin, ya ce magoya bayan APC sun fito da yawa saboda wani shirin tallafi da ka gudanar.
“An yi gangamin ne a ranar Talata da sunan shirin ba da tallafi, wanda sama da mutum 9,000 suka halarta.
“Bayan an kammala a ranar Talata sai aka bukaci wadanda suka ci Hajiyata shirin su dawo ranar Laraba (jiya) domin karbar kayan tallafi,” in ji shi.
’Yan APC ne suka kai mana hari —Ayarin Atiku
Kakakin Atiku, Paul Ibe, ya yi zargin cewa matasan da suka kai wa motocin manyan mutane da ke hanyarsu ta zuwa taron PDP hari suna dauke ne da tutocin APC.
“APC a Jihar Borno ta tura magoya bayanta su kai hari ga bakinmu da suka ziyarci Fadar Shehun Borno a hanyarsu ta zuwa wurin taron.
“APC ta saba irin wannan kidahumacin, amma ta kwana da sanin cewa shure-shure ba zai hana ta mutuwa ba.
“Kaduwarta da ganin yawan mutanen da suka fito ne ya sa take neman razana su kada su halarci taron, wanda hakan ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
“Haka suka yi a lokacin taronmu a Jihar Kaduna, don haka muke jan hankalin masu ruwa-da-tsaki wajen tabbatar da zabe cikin lumana game da take-taken APC na hautsina tarukanmu na yakin neman zabe, musamman a yankin Arewa,” in ji kakakin na Atiku.
Labarin kanzon kurege ne —’yan sanda
A martaninta ga zargin harin, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta ce labarin da PDP ke yadawa karya ce tsagwaronta.
Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Sani Kamilu Muhammed ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, Abdu Umar, da kansa ya je ya duba wajen.
Ya ce “Karya ce tsantsagwaronta ake yadawa domin tunzura mutane da kawo cikas ga tsaron Jihar Borno da ma Najeriya.
“An gudanar da taron yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali da cikakken tsaro.
“’Yan sanda sun raka dan takarar da magoya bayansa zuwa Fadar Shehun Borno inda ya kai gaisuwar ban girma; daga nan kuma suka yi musu rakiya har suka fice daga garin.”
Sai dai ya bayyana cewa ’yan sanda sun tsare wani matashi mai shekara 32 da ta yi kokarin tare ayarin motocin a kan titin Airport Road.
“Yana hannun ’yan sanda da dutsen da ke hannunsa a matsayin shaida,” kamar yadda ya bayyana.
PDP ta shirya harin —Gwamnatin Borno
Da take martani kan zargin, Gwamnatin Jihar Borno ta zargi PDP da shirya harin domin neman a tausaya mata.
Kakakin Gwamna Babagana Zulum, Malam Isa Gusau, ya ce babu dalilin da APC za ta kai wa PDP hari a Borno, domin PDP ba ta da wani farin jini a jihar.
“Gwamna Babagana Zulum yana kyamar bangar siyasa, shi ya sa ya koya musu sana’o’in dogaro da kai.
“Ya kashe sama Naira biliyan biyu wajen koya wa tsofaffin ’yan bangar siyasa san’oin dogaro da kai kuma yanzu suna can suna yin sana’o’insu na neman abinci.
“Ban san daga inda aka samu wannan labarin ba, amma na fara zargin PDP ne ta shirya shi domin biyan bukatar siyasa.
“Da farko Dino Melaye ya ce ’yan bindiga ne suka kai musu hari, da suka ga karyar tasu ba ta samu shiga ba, sai suka dawo suka ce an kai musu farmaki. To wa ya kai musu?”
Daga: Sagir Kano Saleh & Ismail Mudashir (Abuja), Hamisu K. Matazu & Olatunji Omirin (Maiduguri)