2023: Ina da yakinin za a yi sahihin zabe —Jega
Jega ya ce yana da yakinin Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe a 2023 duk da kalubalen da take fuskanta.
Tsohon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa(INEC), Farfesa Atahiru Jega, ya ce yana da yakinin Najeriya za ta gudanar da sahihin zabe a 2023 duk da kalubalen da take fuskanta.
Jega ya bayyana hakan ne a wajen taron karrama Farfesa Adele Jinadu da aka gudanar a Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023
- Samun man fetur a Arewa babbar nasara ce
Ya ce, duk da hare-haren da ake kai wa cibiyoyin INEC da kuma tashin-tashinar yakin neman zaben da ake gani, yana da tabbacin hakan ba zai hana gudanar da ingantaccen zabe ba a badi.
Ya kara da cewa, duk da dai yana ji wa sakamakon zaben tsoro, amma yana da yakinin a kan makomar kasar.
Haka nan, ya ce duk da abubuwa marasa dadi da wasu shugabannin siyasa ke jagorancin aikatawa, yana fatan tsabtataccen zabe zai samu a kasar a 2023.
(NAN)