2023: Ko babu goyon bayan Wike za mu ci zabe —PDP
Bwala ya jaddada cewar Atiku zai hada kan Najeriya domin ci gaban kasa.
Jam’iyyar PDP ta ce ko babu goyon bayan gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, tana da yakinin lashe zaben Shugaban Kasa na 2023.
Kakakin Kwamitin Yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a matsayin gugar zana ga Gwamna Wike da sauran ’yan kanzaginsa.
- ‘Surukata ce ta roki in yi wa ’yarta ciki kafin na aure ta’
- Dan bindiga ya harbe mutum 10 a kantin sayar da kaya a Amurka
Tun bayan kammala zaben tsayar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ne Gwamna Wike da takwarorinsa da aka fi sani da ‘G5’ suka shiga takun saka da shugabancin jam’iyyar.
Wike ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar a zaben, amma ya yi ikirarin cewa ba a gudanar da zaben yadda ya kamata ba sannan ya dage kan cewar lallai sai shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus daga mukaminsa.
Sai dai Bwala a wata hira da ya yi da Gidan Talabijin na Channels, ya yi watsi da matsayar da Wike da sauran gwamnonin suka rika, inda ya ce babu abin da jam’iyyar ta sa a gaba a yanzu face shirin lashe zaben Shugaban Kasa na badi.
“Jam’iyyarmu a shirye take ta lashe zaben. Rashin goyon bayan wike ba zai shafe mu ba.
“Don haka, idan za mu yi nasara da kuri’a miliyan tara ko kuri’a miliyan takwas, don mun samun ragin wasu ‘yan kuri’u ba zai shafe mu ba,” kamar yadda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
“Nasara tana tare ne ga Ubangiji, kuma za mu iya yin hasashen nasarar da za mu samu tun kafin shiga zabe.
“Mun ga abin da ya faru a Osun, inda wasu ‘ya’yan jam’iyyarmu suka yi wa jam’iyyar zagon kasa a jihar.
“Amma me ya faru? Sanatan mai yin rawa [Ademola Adeleke] ya kai ga samun nasara saboda jama’a sun bukaci kawo sauyi a jihar.
“Saboda haka wannan shi ne abin da muke kallo tun kafin shiga zabe.”
Bwala ya kuma yi ikirarin cewa gwamnan Jihar Ribas, Wike ne ya yi sanadin ficewar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da gwamna Dave Umahi da sauransu daga PDP.
Amma ya ce Atiku ya kuduri aniyar hada kan Najeriya duk da rikicin da ke cikin jam’iyyar.