2023: Kotu ta hana INEC dakatar da rajistar masu zabe
SERAP ce dai ta maka INCE a gaban kotun tun da farko
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin wucin-gadi da ya hana Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) dakatar da rajistar masu zabe daga ranar 30 ga watan Yunin 2022.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Mobolaji Johnson ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin, bayan sauraron karar da kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a ayyukan gwamnati ta SERAP ta shigar a gabanta.
SERAP dai ta maka INEC ne a gaban kotun saboda kin amincewar da ta yi ta tsawaita wa’adin yi wa masu zaben rajista.
Ta dai bukaci kotun ne da ta ayyana matakin hukumar zaben a matsayin wanda ya saba wa Kundin Tsarin Mulki sa dokokin kasa da kasa kuma yake kokarin tauye hakkin masu zabe.
A cikin kunshin karar dai da SERAP tare da wasu kungiyoyin fararen hula guda 185 suka shigar, sun bukaci a bayar da umarnin da zai dakatar da INEC daga aniyar tata, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na karshe.
Mai Shari’a Mobolaji dai ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa nan da ranar 29 ga watan Yunin 2022 domin yanke hukunci.
SERAP dai ta ce ta shigar da INEC karar ce saboda yadda ta kara wa jam’iyyu wa’adin gudanar da zabukansu na fitar da gwani, amma ta ki kara na masu rajista wanda zai kare ranar 30 ga watan na Yuni.